Gwamnonin APC za su sa kafar wando daya da Mala Buni kan boyayyen shirin da yake yi

Gwamnonin APC za su sa kafar wando daya da Mala Buni kan boyayyen shirin da yake yi

  • Ana zargin kwamitin Gwamna Mai Mala Buni bai da niyyar shirya zaben shugabannin jam’iyyar APC
  • Mai Mala Buni ya samu goyon bayan wasu Gwamnonin APC da Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN
  • Gwamnan ya shantake a kujerar shugaban APC na kasa, har ya fara hangen mataimakin shugaban kasa

Abuja - Akwai alamun da ke nuna cewa shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni yana kokarin dakatar da zaben shugabannin jam’iyya.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2022 cewa Mai Mala Buni yana da goyon bayan gwamnoni; Atiku Bagudu da Badaru Abubakar.

Ana kuma zargin cewa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami yana cikin wadanda ke marawa kwamitin Mala Buni baya don a daga zaben da za ayi.

Jaridar tace ana tunanin Mala Buni na neman dabarar da zai yi ya cigaba da zama a kan kujerar shugaban jam’iyya har su fitar da ‘dan takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

Wani daga cikin manyan ‘yan APC ya shaidawa Punch cewa gwamnan na Yobe bai so ayi zaben shugabannin saboda yana neman mataimakin shugaban kasa.

Ana kokarin hana zabe

Da yake magana a Abuja, shugaban kungiyar Progressive Governors’ Forum, Salihu Lukman, yace akwai wasu masu kokarin ganin an hana ayi zaben shugabanni.

Sai dai gwamnonin jam’iyyar APC da-dama sun fahimci inda ya dosa, kuma sun fara tunanin taka masa burki a zaman da za su yi ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Gwamnonin APC
Wasu Gwamnonin APC Hoto: www.arise.tv
Asali: UGC

The Nation ta ce hakan ya sa gwamnonin APC suke neman Muhammadu Buhari ya tsoma baki.

Shirin yakar Tinubu

Ana ganin Bola Tinubu ya tada hankalin mutanen Mala Buni bayan ya bayyana niyyar neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ta APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso, da mutane 10 da za su iya bayyana niyyar tsayawa takara bayan Tinubu

Lissafin gwamna Mala Buni shi ne APC ta tsaida ‘dan takarar shugaban kasa na 2023 ta hanyar maslaha, ba tare da abin ya kai ga an yi zaben fitar da gwani ba.

Ganin yadda wasu tsirararun gwamnoni da ba su wuce uku ba da AGF ke tsara yadda za a kauracewa zaben fitar da gwani, Tinubu ya yi shirin rusa shirinsu.

Wani gwamna da ake ganin yana tare da Buni shi ne Dr. Kayode Fayemi. Ana zargin tsohon Ministan yana harin takarar shugabancin Najeriya a karkashin APC.

Gwamnoni sun dare 3 a APC

A watan gobe ake sa rai kwamitin Gwamna Mai Mala Buni zai shirya zaben shugabannin APC na kasa. Sai dai a daidai wannan lokaci, babu tabbacin za ayi zaben.

Gwamnonin jihohin da ke karkashin APC sun bangare inda wasu suke goyon bayan Bola Tinubu, wasu na tare da wani abokin aikinsu da ke neman shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Zaben shugabannin jam’iyyar APC ya jawo sabani, kan Gwamnonin Jihohi ya rabu gidaje 3

Asali: Legit.ng

Online view pixel