Jerin fitattun Sanatoci 10 da suka ci zaman benci a Majalisar Dattawa a shekarar 2021

Jerin fitattun Sanatoci 10 da suka ci zaman benci a Majalisar Dattawa a shekarar 2021

  • Yayinda zaben 2023 yake gabatowa, akwai wasu Sanatoci da ba a jin duriyarsu a Majalisar Dattawa
  • Daga cikinsu akwai tsofaffin gwamnoni irinsu Ibrahim Shekarau da Aliyu Magatakarda Wammako
  • Haka zalika ana kukan an rasa inda Sanata Chimaroke Nnamani da kuma Peter Nwobaoshi suka shiga

1. Chimaroke Nnamani

A jerin da jaridar Order Paper ta fitar na ‘yan majalisar dattawan da suke cin zaman benci akwai Sanatan PDP mai wakiltar Enugu na gabas, Chimaroke Nnamani.

2. Nora Dadut

Tun da Nora Dadut ta canji Sanata Ignatius Longjan bayan rasuwarsa a majalisar dattawa a 2020, ba a jin labarinta duk da cewa Farfesa ce a jami'a kafin shiga siyasa.

3. Kola Balogun

Kola Balogun ne ya doke tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi a zaben majalisar dattawan 2019 amma Balogun yana cikin ‘yan majalisar da ba su cewa uffan.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Gwamna a APC ya ware Naira miliyan 200 zai rabawa Daliban Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

4. Ibrahim Gaidam

A shekarar 2010 Ibrahim Gaidam ya zama gwamnan jihar Yobe. Abin da aka fi tuna Sanatan na gabashin Yobe da shi, shi ne kudirin gyara halin ‘Yan Boko Haram.

Sanatoci
Majalisar dattawan kasa Hoto: @NgrSenate/Tope Brown
Asali: Facebook

5. Godiya Akwashiki

Ko da Godiya Akwashiki sabon shiga majalisa ne, shi ne shugaban kwamitin kwadago, bai yi komai ba sai kawo kudirin kafa makarantar kiwon lafiya a kauyensa.

6. Aliyu Magatakarda Wammako

Aliyu Magatakarda Wammako mai wakiltar Sokoto ta Arewa ya na cikin tsofaffin gwamnonin da ake ganin zamansu a majalisar tarayya ba ya amfanar al’ummarsu.

7. Lawan Anka

Sanatan Zamfara na yamma, Lawan Anka ya shiga sahun wadanda ake ganin su na dumama benci duk da kashe-kashe da ta’adin da ‘yan bindiga suke yi a yankinsa.

8. Peter Nwobaoshi

Rahoton Matterarising yace Sanatan Delta ta Arewa, Peter Nwobaoshi ba ya tabuka komai, har ana zargin cewa bai cika halartar zaman da ake yi a majalisa ba.

Kara karanta wannan

Bayan wata da watanni ana rigingumu, Mai Mala Buni ya sasanta rikicin APC a Gombe

9. Bomai Mohammed

Wani Sanata da ba a ji duriyarsa a shekarar 2021 ba shi ne Bomai Mohammed mai wakiltar mazabar Kudancin Yobe, sai dai shi ma a 2019 ya fara zuwa majalisa.

10. Ibrahim Shekarau

Na karshe a jerin na mu shi ne Malam Ibrahim Shekarau, babu mamaki don sunansa ya shiga nan domin shi ma ya taba yin gwamna na shekaru takwas a jihar Kano.

Sai Yahaya Bello 2023?

A yau ne ake jin cewa wasu fastoci 100 da jagororin coci 1000 za su dukufa da addu’a da azumi domin ganin gwamna Yahaya Bello ya karbi mulkin Najeriya a 2023.

Jonathan Praise wanda ya jagoranci addu'o'in yace Bello ne zai zama magajin Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel