Mai neman takarar Gwamna a APC ya ware Naira miliyan 200 zai rabawa Daliban Kano

Mai neman takarar Gwamna a APC ya ware Naira miliyan 200 zai rabawa Daliban Kano

  • Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya yi alkawarin zai kashe N200m a kan yaran Kano da suke karatu
  • Duk wani dalibi daga jihar Kano da yake manyan makarantu zai iya tashi da gudumuwar N20, 000 a bana
  • Gidauniyar AA Zaura za ta raba wadannan miliyoyi a shekarar 2022 domin a bunkasa harkar ilmi

Kano - Daya daga cikin wadanda ake ganin za su nemi takarar gwamna a APC a jihar Kano, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, zai raba kyautar N200m.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa Abdulsalam Abdulkarim Zaura zai raba wadannan kudi ne ga ‘yan asalin Kano da suke karatu a manyan makarantu.

Gidauniyar AA Zaura Foundation ta ware N200m domin yaran Kano da suke makaranta a jami’o’i da makarantun koyon aiki da kwalejojin ilmi a Najeriya.

Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya cika alkwarin da ya yi a jawabin murnar shiga sabuwar shekara ta 2022 da ya fitar wanda ya shiga hannun NNN.

Kara karanta wannan

Jerin fitattun Sanatoci 10 da suka ci zaman benci a Majalisar Dattawa a shekarar 2021

Alkawarin AA Zaura ya cika

“Kamar yadda na yi alkawari a sakon shiga sabuwar shekara da na yi, a shekarar nan za mu kai tallafinmu na AA Zaura Foundation zuwa wasu wuraren.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Daga cikin alkawuran da muka dauka sun fara tabbata. Sanin kowa ne cewa ba a samun cigaba sai da ilmi, don haka zan tallafawa daliban Kano 10, 000.”
Gidauniyar AA Zaura Foundation
Tallafin Gidauniyar AA Zaura Foundation Hoto: @AAZAURASOCIALMEDIA
Asali: Facebook

“Zan tallafawa daliban Kano da suke karatu a makarantun gaba da sakandare na gwamnati. Zan ba kowa gudumuwar kudi N20, 000.” – Alhaji AA Zaura.

A ziyarci shafin yanar gizo

Za a samu bayanin yadda za a zakulo wadanda za a ba kyautar kudin a shafin gidauniyar a yanar gizo a: https://aazaura.org.ng/education-support-fund/

Kamar yadda Attajirin ya bada sanarwa, za a cike fam a saukake wanda ba zai ci wa mutum fiye da minti biyar ba, dole ne sai mutum ya nuna takardunsa.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun tafka barna a Zariya, sun kashe mutane sun saci dabbobi

Akwai bukatar mai neman wannan taimako ya ziyarci shafin, sai ya nuna takardarsa na zama ‘dan Kano da kuma takardar shiga makarantar da yake karatu.

Nan gaba gidauniyar za ta taimakawa mata miliyan daya da kuma matasa miliyan biyu a Kano.

Ya kashe mahaifinsa

Dazu kun ji cewa da wani Abubakar Mohammed Buba ya fada hannun jami’an tsaro, ya tona kansa da kansa, yace shi ya bada kudi a kashe mahaifinsa.

Abubakar Buba ya biya wani abokinsa N100, 000 ya sheka da tsohonsa barzahu, abin da ya sa ya yi wannan aiki kuwa shi ne saboda ya yi maza ya ci gado.

Asali: Legit.ng

Online view pixel