Kwanaki kasa da 30 suka rage, har yau babu tabbacin APC za ta shirya zaben shugabanni

Kwanaki kasa da 30 suka rage, har yau babu tabbacin APC za ta shirya zaben shugabanni

  • A watan Fubrairun 2022 ake sa ran cewa jam’iyyar APC za ta shirya zaben shugabanninta na kasa
  • Har zuwa yanzu babu abin da ke nuna shugabannin APC sun fara shirin gudanar da wannan zaben
  • Ana rade-radin wasu masu rike da madafan iko su na kokarin ganin an yi watsi da wannan zabe

Abuja - Ba dole ba ne zaben shugabannin APC na kasa da aka dade ana jira ya kankama. Daily Trust tace wasu na kokarin karbe ikon jam’iyyar saboda zaben 2023.

Wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar APC mai mulki da ‘yan takara sun fara kokawa a game da rashin shirin kwamitin Mai Mala Bunin a shirya zaben shugabanni.

Rahoton yace makonni shida bayan an bada sanarwar za a gudanar da zaben shugabanni na kasa a watan Fubrairu, babu wani abin da gwamna Mai Mala Buni ya yi.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

Haka zalika shugabannin rikon kwarya ba su tsaida ranar da ake sa ran za a shirya wannan zabe ba.

Bugu da kari, jaridar Daily Trust tace ba ayi magana a game da wurin da za ayi wannan taro ba. Wannan ya kara cusa ‘ya ‘yan jam’iyyar su na zaune a cikin duhu.

Shugabannin APC
Taron APC NEC a Abuja Hoto: @ Bashir Ahmaad
Asali: UGC

Ya ake ciki?

Mala Buni da ‘yan majalisarsa da za su gudanar da wannan zabe ba su tsaida ranar da majalisar koli ta NEC za tayi zama domin a tsara yadda za ayi zaben ba.

Kawo yanzu kwamitin rikon kwarya na gwamnan Yobe, Mai Mala Buni bai kafa kwamitocin da za su yi aikin yada labarai da kason kujeru a zaben na 2022 ba.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa akwai wasu gungu a fadar shugaban kasa da gwamnonin jihohi da suke kokarin ganin an fito da shugabanni ba da zabe ba.

Kara karanta wannan

Siyasa: Manyan rigingimun da suka aukawa jam’iyyun PDP da APC a shekarar 2021

Wadannan masu iko a jam’iyyar APC su na so ne a tsaida ‘yan majalisar ta NWC ta hanyar maslaha. Hakan ba zai yi wa masu shirin tsayawa takara dadi ba.

Masu harin kujerar Buni

Masu neman kujerar shugaban jam’iyya sun hada da; Abdulaziz Yari, Sanata Ali Modu Sheriff; Malam Isa Yuguda, George Akume, Saliu Mustapha, da Sani Musa.

Sai kuma irinsu Sanatan Nasarawa, Tanko Al-Makura, Sunny Moniedafe da Mohammed Saidu Etsu.

Kwankwaso zai dawo APC

Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo batun komawarsa APC, ya ce makomar PDP yanzu ta na ga kotun koli inda za yanke hukunci tsakanin jam’iyya da Uche Secondus.

Tsohon gwamnan yace komai na iya faruwa, sannan ya bada muhimmiyar shawarar da yake ganin za ta taimaki jam’iyyu, yace burinsa a samu shugaba na gari a 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel