Siyasa: Manyan rigingimun da suka aukawa jam’iyyun PDP da APC a shekarar 2021

Siyasa: Manyan rigingimun da suka aukawa jam’iyyun PDP da APC a shekarar 2021

  • Manyan jam’iyyun siyasan Najeriya APC da PDP sun samu kansu a matsaloli iri-iri a shekarar nan da za ta wuce, jaridar Daily Trust ta kawo wasu a cikinsu
  • Irin wadannan rigingimu na cikin gida ba farau ba ne a siyasar kasa ko Duniya. Wadannan rikici ne suka yi sanadiyyar da aka samu ‘yan taware a wasu jihohi
  • An samu wasu manyan ‘yan siyasa da suka sauya-sheka a shekarar nan, kusan babu wanda komawarsa APC a 2021 ta bada mamaki irin Femi Fani-Kayode

Ga wasu daga cikinsu nan kamar haka:

1. Babban gangamin APC

Tun da Mai Mala Buni ya karbi jam’iyyar APC na rikon kwarya daga hannun Adams Oshiomhole, har yanzu ana ta kai-komo a kan zaben manyan shugabanni na kasa.

2. Zaben shugabannin APC

Akwai kuma zaben shugabannin APC na matakin mazabu, kananan hukumomi da jiha, wanda shi ma ya jawo rabuwar kai tsakanin gwamnoni da wasu ‘yan jam’iyya.

Kara karanta wannan

2023: Babban faston Najeriya ya bayyana wanda zai gaji Buhari

Rahoton yace irin wannan rikicin na cikin gida ya fi kamari a jihohi irinsu Kano, Ekiti, Ogun, Oyo, Cross River, Akwa Ibom, Delta, Osun, Abia, Zamfara da jihar Kwara.

Jam’iyyun PDP
Zaben shugabannin PDP Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

3. Rikicin shugabancin PDP

Ita kan ta jam’iyyar PDP ta na ta fuskantar matsaloli tun bayan da aka dakatar da shugaban jam’iyya na kasa, Prince Uche Secondus daga mazabarsa a jihar Ribas.

Duk da Prince Uche Secondus ya shigar da jam’iyya kotu, PDP tayi zaben shugabanninta na kasa.

4. Rigigumun PDP a jihohi da shiyyoyi

Baya ga rikicin shugabanni na NWC, akwai rassoshin jam’iyyar PDP da ba a zaman lafiya a jihohi. Sannan har yau an gagara zaben shugabannin PDP na wasu yankunan.

5. Sauya-sheka

A karshe kuma akwai fama da canza sheka da wasu ‘yan siyasa suke yi saboda rashin gamsuwa da halin da jam’iyyarsu ta ke ciki, ko kuma kwadayin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Manyan ayyuka 5 da wasu gwamnonin Najeriya suka aiwatar a 2021

A dalilin haka ne PDP ta rasa wasu gwamnoninta zuwa APC a 2021. Sannan irinsu Femi Fani-Kayode, Barnabas Gemade, da Yakubu Dogara sun bar tafiyar PDP.

Rikicin siyasa a Imo

A jihar Imo kuwa surukin tsohon Gwamna kuma Sanatan Imo, Rochas Okorocha, Uche Nwosu yace gwamnatin jihar ta na zargin ya na taimakawa ‘yan ta’adda.

Uche Nwosu ya musanya wannan zargi, yace bai da wata alaka da ‘yan bindiga. Har yanzu dai bangaren Okorocha ba su ga maciji da na Hope Uzodinma a Imo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel