Yanzu-Yanzu: Bashir Tofa, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 1993, Ya Rasu

Yanzu-Yanzu: Bashir Tofa, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 1993, Ya Rasu

  • Allah ya yi wa Alhaji Bashir Tofa, dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 1993, da ya fafata da MKO Abiola rasuwa
  • Marigayin ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Aminu Kano, AKTH, a Kano bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • An haifi Tofa ne a shekarar 20 ga watan Yunin 1940 kuma yana daga cikin wadanda suke bada shawarwari kan yadda za'a warware matsalolin da ke adabar Najeriya

Jihar Kano - Alhaji Bashir Tofa, ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban kasa a zaben 1993, wanda ake yi wa kallon zabe mafi adalci a Najeriya, ya rasu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: Bashir Tofa, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Zaben 1993, Ya Rasu
Alhaji Bashir Tofa, tsohon dan takarar shugaban kasa na NRC ya rasu. Hoto: Daily Trust

A cewar majiyoyi daga yan uwansa, Tofa ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Aminu Kano, AKTH, a safiyar ranar Litinin bayan gajeruwar lafiya, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige Jigon APC har lahira jim kadan bayan ya kammala addu'o'i

'Yan uwansa sun tabbatar da rasuwarsa

Da ya ke tabbatar da rasuwarsa, dan uwan marigayin ya ce, "Alhaji Bashir Tofa ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya."

Ya ce ya shafe kwanaki a sashin bada kulawa ta musamman na asibitin kuma ya fara samun sauki. Amma daga bisani ciwon ta ci karfinsa.

Hakazalika, Ɗaya daga cikin ƴaƴan Tofa, wacce kwanaki uku da suka gabata ta musanta rasuwarsa yayin da labarin ya bazu a dandalin sada zumunta, ta tabbatar da rasuwarsa a safiyar ranar Litinin.

Kafin rasuwarsa, Tofa na daga cikin wadanda suke tofa albarkacin bakinsu kan al'amuran da ke damun Najeriya musamman yadda za a warware batun rashin tsaro.

Tofa, ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar National Republican Convention, NRC, a zaben 1993, ya ƙara da marigayi MKO Abiola na jam'iyyar Social Democratic Party, SDP.

Kara karanta wannan

Shekaru kadan bayan nada shi sarauta, fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya

Amma, Shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya soke zaben.

An haifi Tofa ne ranar 20 ga watan Yunin 1947.

Ku saurari ƙarin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel