Yadda mutuwar kanin Kwankwaso da auren diyar Shekarau suka sauya lissafin siyasar Kano

Yadda mutuwar kanin Kwankwaso da auren diyar Shekarau suka sauya lissafin siyasar Kano

Lamurra biyu, mutuwa da biki a jihar Kano sun sauya lissafin siyasa na jihar Kano kafin zuwan zaben 2023, wanda hakan yasa masu kiyasi ke kallon ketowar alfijir na sabon tarihi.

Mutuwar Alhaji Inuwa Kwankwaso, kanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da auren diyar Sanata Ibrahim Shekarau, dukkansu tsoffin gwamnonin jihar, su ne suka kawo sabon hadin kai a tsakanin manyan shugabannin siyasar jihar Kano.

Yadda mutuwar kanin Kwankwaso da auren diyar Shekarau suka sauya lissafin siyasar Kano
Yadda mutuwar kanin Kwankwaso da auren diyar Shekarau suka sauya lissafin siyasar Kano. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kwankwaso da Shekarau dukkansu sun shugabanci jihar na tsawon shekaru takwas-takwas, yayin da gwamnan yanzu, Abdullahi Umar Ganduje, ya ke da watanni 17 kafin cikar mulkinsa wa'adi na biyu.

Sai dai kuma, tsofaffin gwamnonin biyu suna da wasu abubuwa masu kamanceceniya dangane da Kano da Najeriya fiye da tsarin shugabancin cibiyar kasuwancin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Babu shakka an yi wa Ganduje warwas a zaben 2019, masu iko suka makala wa Kano

A yayin da Kwankwaso ya taba rike ministan tsaro a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Shekarau ya yi ministan ilimi yayin mulkin Goodluck Jonathan.

Hakazalika, Kwankwaso ya wakilci mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019, mukamin da a halin yanzu ya ke hannun Shekarau.

Har ila yau, dukkansu ana kallonsu a matsayin 'yan siyasa masu karfin iko a siyasar Kano kuma ana matukar mutunta su sakamakon yawa da jajirtattun mabiyansu.

Wannan kuwa babu shakka ya na da alaka da zaman Shekarau gwamnan jihar Kano a 2003, yayin da ya hana Kwankwaso zarcewa bayan cikar wa'adin mulkinsa na farko.

Tun daga nan, siyasar Kano ta rabu tsakanin wadannan masu karfin iko. Kuma gwamnan yanzu, Abdullahi Umar Ganduje na hannun daman Kwankwaso ne tun 1999 kafin su raba jiha a zaben 2015 inda aka samo tsagin Gandujiyya a jihar.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun farmaki manyan sarakunan jihar Bauchi

Ganduje ya rike mataimakin Kwankwaso na tsawon shekaru takwas kuma ya kasance tare da shi har a lokacin da ya ke ministan tsaro.

Tun bayan rabuwarsu, Ganduje da Kwankwaso ba su sukar juna, sai dai mabiyansu ba su sassautawa a duk lokacin da suka samu damar yin hakan.

Rasuwar Alhaji Inuwa Kwankwaso ta tashi hankula, wanda hakan yasa Ganduje ya ziyarci tsohon ubangidansa domin yi masa ta'aziyya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, yayin ziyarar Ganduje, tsohon gwamnan ya gayyacesa zuwa kabarin mahaifinsa, Musa Saleh Kwankwaso, wanda ke cikin gidansa da ke Bompai inda suka yi masa addu'a ta musamman.

Bayan addu'ar, an bar abokan hamayyar biyu kuma shugabannin siyasan Kanon inda suka tattauna, Daily Trust ta ruwaito.

Daga bisani, gwamnan ya bayyana shirinsa na sasantawa da Kwankwaso inda ya kwantanta matsalar da ke tsakaninsu da aikin makiya.

Kwankwaso ya aurar da diyar Shekarau

A ranar 24 ga watan Disamba, mazauna Kano da masu sahida sun sha mamamki lokacin da suka ga Kwankwaso a wurin daurin auren Halima Ibrahim Shekarau da Adamu Yusuf Maitama. Karin mamakin shi ne yadda tsohon gwamnan ya bayar da auren Halima.

Kara karanta wannan

Duk kashe-kashen da ake yi na matukar damuna, Buhari ya aike sakon jaje ga yan Najeriya

A sakon sabuwar shekara, Ganduje ya yi magana kan sasanci da Kwankwaso da tsagin Shekarau

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya magantu kan bukatarsa na sasantawa da abokin hamayyarsa, tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso da tsagin APC karkashin shugabancin Sanata Ibrahim Shekarau.

A sakon sabuwar shekara, wanda kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba yasa hannu a ranar Juma'a, Ganduje ya ce zai sadaukar da sabuwar shekarar wurin tabbatar da sabon tsarin zaman lafiya da sasanci tsakanin masu ruwa da tsakin jam'iyyun siyasa a jihar da kasar baki daya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, duk da gwamnan bai kira sunayen 'yan siyasan ba, takardar ta jaddada bukatar shugabannin kungiyoyin siyasa na jihar da su hada kai domin kawo sabon tsari a siyasar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel