Tsohon Gwamna Kwankwaso ya bada satar-amsar yiwuwar sulhu da abokan gaba kafin 2023

Tsohon Gwamna Kwankwaso ya bada satar-amsar yiwuwar sulhu da abokan gaba kafin 2023

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo zancen da ake ta yi na yiwuwar yin sulhu
  • Rabiu Musa Kwankwaso yace haduwar kan ‘yan adawa a Kano domin ceto jama’a abu ne mai kyau
  • ‘Dan siyasar ya yi kira ga mabiya musamman ‘Yan Kwankwasiyya su zama masu biyyayya a kullum

Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace abu ne mai kyau a hada-kai, har ya na fatan ‘yan siyasa za su yi koyi da irin wannan saboda a iya ceto al’umma.

Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi wata hira da gidan talabijin na Rahma TV Kano a ranar Alhamis, 23 ga watan Disamba, 2021.

“Mu na fatan duk ‘yan siyasa su koyi irin wadannan. Sako na biyu shi ne; ‘yan siyasa, musamman ‘Yan Kwankwasiyya, su yi hattara a kan irin abubuwan da ke faruwa”

“Yanayin siyasa da mu ke ciki mai muhimmanci ne, wanda ba kowa ne zai iya fahimta ba."

- Rabiu Kwankwaso

Sanata Kwankwaso yace ‘yan siyasa na yin kuskure, su dauka cewa sun gama daukar darasi saboda sun rike mukaman kwamishinoni, ministoci ko shugaban kasa.

Tsohon Gwamna Kwankwaso da Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

“Sai mutum ya dauka ya san komai, ya iya komai, kuma watakila ya na da abin da zai koya.”
“Siyasa hawa bakwai ce daga yanzu zuwa zabe, yanzu mu na hawa na shida, lokacin zabe za a kai hawa na bakwai, wannan hawa ne mai bukatar matukar gogewa.”
“Mu na kira ga magoya-baya a kana bin da mu ka sag aba na saita siyasa a Kano da Najeriya. Ka da mutane su rika sa baki, su na fadin abin ba su fahimta ba.”

- Kwankwaso

Kwankwaso yace a halin da ake ciki sun yi tsari da ke nuna alamun nasarar da aka dade ba a ga irinta ba, don haka ya yi kira ga magoya baya su zama masu biyayya.

‘Dan siyasar yace abin da yake kan magoya baya shi ne su bada shawara a inda aka bukata, sai su bi umarnin jagora wanda shi ne zai dauki shawarar da za ta fi bullewa.

A hirar ta sa, Kwankwaso yace sai mai zurfin tunani zai fahimci abin da zai faru kafin zaben 2023, don haka ya yi gargadi a kan sakin baki a rika surutai marasa kan gado.

“Idan ka na da shugabanci, komai tudunka a siyasa, daga na ka tudun ne na shi ya fara, musamman da za mu shiga 2022, lokacin da ake bukatar kwarewa.”

Kwankwaso ya hadu da Shekarau?

Kun ji cewa bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi masa ta’aziyya har gida, Rabiu Kwankwaso zai bada auren ‘Yar Malam Ibrahim Shekarau a ranar Juma'ar nan.

Bayan sallar Juma’ar yau, Halima Ibrahim Shekarau za ta auri sahibinta, Adamu Yusuf Maitama a masallacin Umar Bn Khatthab, Kwankwaso ne zai zama waliyyinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel