Siyasar Kano ta rikide, a yau Kwankwaso zai aurar da ‘Diyar cikin abokin adawarsa, Shekarau

Siyasar Kano ta rikide, a yau Kwankwaso zai aurar da ‘Diyar cikin abokin adawarsa, Shekarau

  • Sanusi Bature Dawakin-Tofa yace Rabi'u Musa Kwankwaso zai bada auren Halima Shekarau an jima
  • Za a daura wannan aure ne a yau Juma’a a yayin da siyasar Kano ta ke canza salo a halin yanzu
  • Sanata Kwankwaso ya na cikin manyan abokan adawar magajinsa, Ibrahim Shekarau a jihar Kano

Kano - A yammacin Alhamis, 23 ga watan Disamba, 2021, Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa Sanata Ibrahim Shekarau zai aurar da wata ‘yarsa a yau.

Abin mamaki game da wannan aure da Sanatan Kano ta tsakiya zai bada shi ne, tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau ne zai zama waliyyin wannan ‘diyar ta sa.

A wani rahoto da ya fito daga bakin Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Ahmad Lawan za su zama iyayen amarya.

Kara karanta wannan

Bayan Legas, an samu Gwamnan Arewa da zai gwangwaje ma’aikata da kudin karshen shekara

Malam Sanusi Bature Dawakin-Tofa wanda ya yi aiki da Injiniya Abba Kabiru Yusuf a lokacin da ya fito takarar gwamnan Kano yace za a daure auren a yau.

Wannan budurwa, Halima Shekarau za ta auri sahibinta, Adamu Yusuf Maitama. Za a daura auren ne bayan an sauko sallar juma’a a masallacin Umar Bn Khattab.

Kwankwaso da Shekarau
Ibrahim Shekarau a gidan jagoran Kwankwasiyya Hoto: mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar da aka fitar

“Gobe Juma’a, 24 ga watan Disamba, 2021, idan Allah (SWT) ya kai mu, Rabi'u Musa Kwankwaso da shugaban majalisa, Dr. Ahmad Lawan, za su ba da auren ‘yar Ibrahim Shekarau, Halima (Amira).
Halima Ibrahim Shekarau za ta auri Adamu Yusuf Maitama a masallacin Umar Bn Khatthab da ke kan titin garin Zaria, jihar Kano da karfe 2:00 na rana, bayan sallar Juma’a.”

Tarihin siyasar Kwankwaso v Shekarau

Yayin da Sanata Ahmad Lawan yake shugaban majalisar dattawa, Rabi'u Musa Kwankwaso ya na cikin manyan abokan gaban Ibrahim Shekarau a siyasar Kano.

Kara karanta wannan

Wani mai jinyar karaya ya yi karfin-hali, ya sace motar daukar marasa lafiya a jihar Kano

Malam Ibrahim Shekarau ne ya tika Rabiu Musa Kwankwaso da kasa a lokacin da ya nemi tazarce a zaben gwamnan jihar Kano shekaru 18 da suka wuce.

Lamarin ya juya a zaben 2011 inda Kwankwaso ya karbi mulkin Kano a hannun Malam Shekarau. Dukkaninsu sun rike kujerun Ministoci bayan sun bar gwamnati.

Har ila yau tsohon gwamna Ibrahim Shekarau ne ya sake canzar magajinsa, Kwankwaso a majalisar dattawa bayan jigon na PDP ya hakura da kujerar a 2019.

Za ayi sulhu a Kano?

Kun ji Gwamna Abdullahi Ganduje da sabon abokin rigimarsa, Ibrahim Shekarau duk sun je gidan Rabiu Kwankwaso domin yi masa ta'aziyyar rashin 'danuwansa.

A halin yanzu tsagin tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau sun karbe shugabancin APC a Kano, har an fara hararo sulhi tsakanin Ganduje da Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel