'Yan Najeriya za su fi ganin amfanin Buhari bayan ya sauka daga mulki, Gwamnan arewa

'Yan Najeriya za su fi ganin amfanin Buhari bayan ya sauka daga mulki, Gwamnan arewa

  • Duk da caccakar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke sha akan rashin tsaro, Gwamna Sule ya ce za a yi kewarsa idan ya sauka mulki
  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ne ya bayyana wa manema labarai hakan inda ya ce Buhari ya fadi hakan lokacin da suka hadu
  • Kamar yadda gwamnan ya ce, ya sanar da Buhari cewa sai ya sauka kafin ‘yan Najeriya da dama su gane wasu bangarorin da ya yi kokari

Duk da yadda ‘yan Najeriya da dama suke ta sukar matsalar rashin tsaro da tattalin arzikin Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari, wani jigon gwamnati ya ce ‘yan Najeriya za su yi kewarsa idan ya sauka daga mulki.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yayin hira da manema labaran gidan gwamnati ya fadi hakan bayan haduwarsa da shugaban kasa ranar Talata, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa

'Yan Najeriya za su fi ganin amfanin Buhari bayan ya sauka daga mulki, Gwamnan arewa
'Yan Najeriya za su fi ganin amfanin Buhari bayan ya sauka daga mulki, Gwamnan arewa. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC
“Na sanar da shugaban kasa cewa ‘yan kasa ba za su lura da kokarinsa ba har sai ya sauka daga kujerarsa. Kwanan nan gwamnatin jihar Nasarawa ta sa hannu a yarjejeniya bayan tattaunawa a babban birnin jihar, Lafia, a lokacin manyan jiga-jigan NNPC su na nan,” a cewar Sule.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suke halaka ‘yan Najeriya da dama yayin da su ka yi garkuwa da wasu a kusan kowanne mako a arewacin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da halin tsananin rayuwar da ake ciki, tsadar kayan masarufi ya na ta karuwa.

Sule ya bayyana cewa basu tattauna da Buhari akan tabarbarewar tsaro ba. Sai dai ya ce sun tattauna akan wasu abubuwan da shi.

A cewarsa:

“Mun tattauna da shugaban kasa akan amfani da iliminmu wurin bunkasa matatun gas a Afirka ta yamma wanda ake samowa daga Sagamu zuwa Ikeja don sauran ma’aikatu su amfana.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

“Ga kasa irin Najeriya da ta ke da albakatun ma’adanai, ba na tunanin idan mutum ya ce zai gina kamfanonin gas ba kankanin abu bane. Amma mutane ba za su gane ba har sai ya sauka daga kujerarsa.
“Idan ya sauka, gas din girki ya wadata sannan ababen hawarmu su ka koma amfani da gas, a lokacin ne za a san cewa Buhari ya yi aiki kuma a dinga yi masa fatan alheri.”

Gwamnan ya ce a cikin gidan gwamnatin ya yi wa Buhari godiya akan yadda ya tallafa wurin samar da zaman lafiya a kasar nan.

Ya ce shugaban kasa ya yi kokari kwarai wurin dawo da tsaro a cikin yankinsu, kuma sojojin kasa da sama tare da ‘yan sanda su na yin aiki tukuru wurin bayar da tsaro a kananun hukumomi biyu masu iyaka da Abuja, Toto da Karu.

Ya kara da bayyana farin cikinsa akan yadda Nasarawa ta samu tsaro da kwanciyar hankali, inda ya ce yanzu ana noman rogo da doya sosai a kasar nan, don su ne na biyu.

Kara karanta wannan

Rahoto: Kudurorin gwamnatin Buhari da zasu jefa 'yan Najeriya cikin bakaken wahalhalu a 2022

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel