Mala Buni na fuskantar barazana, Matasan APC sun nemi kotu ta tsige Shugaban Jam’iyya

Mala Buni na fuskantar barazana, Matasan APC sun nemi kotu ta tsige Shugaban Jam’iyya

  • Kungiyar Progressive Youth Movement na APC sun kai karar jam’iyya da INEC a gaban kotu a Abuja
  • Matasan jam’iyyar APC sun ce tsarin mulki bai halastawa gwamna rike shugabanci a jam'iyya ba
  • Baya ga tsige Gwamna Mai Mala Buni, PYM ta na so BOT ta kira ranar zaben shugabanni na dabam

Abuja - Wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar a karkashin kungiyar Progressive Youth Movement (PYM), sun shigar da karar uwar jam’iyyar a gaban kotu.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, 2021, kungiyar Progressive Youth Movement na neman ta kawowa zaben APC cikas.

Matasan su na so kotu ta tsige kwamitin rikon kwarya da shirya zabe wanda Mai Mala Buni yake jagoranta. Sannan ta na so BOT ta kira zaben shugabanni.

Kara karanta wannan

Gwamnatin APC ta 'yan koyo ne, mu ne za mu iya gyara Najeriya, inji jam'iyyar PDP

Rahoton yace Progressive Youth Movement ta na so Alkali ya hana gwamnan jihar Yobe bayyana kan shi a matsayin shugaban jam’iyyar riko na APC na kasa.

Lauyoyin kungiyar matasan sun hada da jam’iyyar APC mai mulki, hukumar INEC, da gwamna Mai Mala Buni a matsayin wadanda su kare kansu a kotu.

Mala Buni
APC ta na kamfe a 2019 Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Abin da doka da tsarin mulki su ka ce

Masu karar sun kafa hujja da sassa na 13.2 (A)(vii) da na 17(iv) na tsarin mulkin jam’iyyar APC, suka ce ba a halattawa gwamna ya zama shugaba a jam’iyya ba.

Yayin da Mala Buni yake rike da kujerar gwamnan jihar Yobe, Progressive Youth Movement tace bai da damar da zai rike wani mukamin zartarwa a jam’iyya.

Bugu da kari, masu karar sun ce hakan ya sabawa sashe na 183 na kundin tsarin mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Yari Vs Matawalle: Kotu ta yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a Zamfara

A kira sabon ranar zaben shugabanni

Rahoton yace matasan sun kuma roki kotun tarayyar na Abuja ta ba majalisar amintattu watau BOT na jam’iyyar APC dama ta kira wani ranar zaben shugabanni.

Lauyan da ya tsayawa PYM yace sashe na 17(iv) na tsarin mulkin APC ya ba majalisar BOT damar ta kira zabe. Har yanzu dai ba a sa ranar da za a saurari karar ba.

Siyasar Zamfara

A makon nan ne aka ji cewa Kabiru Sahabi-Liman ya koma tsagin Gwamna Bello Matawalle a jam’iyyar APC, inda ya rabu da tsohon mai gidansa, Abdulaziz Yari.

Alhaji Kabiru Sahabi-Liman ya rike kwamishina a lokacin da Abdulaziz Yari yake gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel