2023: Sanatan APC ya shiga cikin masu yi wa Gwamnan Arewa kamfe, yace ya dace da Najeriya

2023: Sanatan APC ya shiga cikin masu yi wa Gwamnan Arewa kamfe, yace ya dace da Najeriya

  • Smart Adeyemi ya na goyon bayan gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya zama Shugaban kasa a 2023
  • A ra’ayin Sanata Smart Adeyemi, Gwamna Yahaya Bello ya nuna zai iya rike gwamnatin tarayya
  • ‘Dan majalisar ya bayyana haka a bikin kaddamar da tafiyar Global Alliance of Progressive Professionals

Abuja - Smart Adeyemi, Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, ya bayyana goyon bayansa ga Yahaya Bello a zaben shugaban kasan 2023.

‘Dan majalisar dattawan ya bayyana wannan ne a wajen bikin kaddamar da wata kungiyar magoya-baya ta Global Alliance of Progressive Professionals.

PM News tace wannan kungiya ta GAP3 ta na yi wa Gwamna Yahaya Bello yakin neman zabe.

Sanata Smart Adeyemi ya yabi matasan da suka kirkiro wannan tafiya ta goyon bayan gwamnan jihar Kogi, Bello ya tsaya takarar kujerar shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Buhari zai gyara Najeriya tsaf kafin ya sauka a mulki a zaben 2023, inji Sanata

Adeyemi ya jero wasu daga cikin halaye da baiwar Yahaya Bello da suka sa zai yi kyau da shugaban kasa, daga ciki akwai basira da kuma hangen nesarsa.

Gwamnan Kogi
Yahaya Bello yana neman tazarce a Kogi Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin da Smart Adeyemi ya fada

“An karfafe mu sosai da ganin matasa masu tasowa sun yarda da gwamnatin (Yahaya Bello), shiyasa mu ka zo domin mu mara masu baya.”
“Domin hakarsu ta cin ma ruwa a kowane sako da kwararon kasar nan, su yi bayanin irin alherin da suka gani tattare da gwamna Bello.”
“Gwamnan matashi ne mai matukar hangen nesa, ya na da baiwar jagoranci, kuma ya na da basira, ya nuna haka a Kogi.” – Smart Adeyemi.

Inda Bello ya zarce sa'a - Adeyemi

A cewar Sanata Adeyemi, yanzu jihar Kogi ta na cikin jihohin da su ka fi kowane zaman lafiya a fadin Arewacin Najeriya, baya ga cigaba ta fuskar halin rayuwa.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

Jaridar ta rahoto Sanatan yana cewa gwamnatin Bello ta taimaka wajen jawo kamfanonin kasashen waje su zuba hannnun jari, abin da Najeriya ta ke nema.

Hukumar dillacin labarai ta NAN ta ce an kaddamar da tafiyar GAP3 da Ahmed Chikaji a matsayin shugaban kungiya, an nada jagorori a duk jihohin Najeriya.

Anya APC za ta mika mulki?

Babban jigo a PDP, Cif Raymond Dokpesi, yace babu tabbacin APC za ta mika mulki idan ta fadi zaben shugaban kasa a 2023, kamar yadda Goocluck Jonathan ya yi.

An ji Raymond Dokpesi yana cewa ba dole ba ne jam’iyyar APC ta yi irin abin da Goodluck Jonathan ya yi da ya sha kashi a 2015, ya sallama mulkin salin-alin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel