Dokpesi: Zai yi wahala APC ta mika mulki a ruwan sanyi idan ta sha kasa yadda Jonathan ya yi a 2015

Dokpesi: Zai yi wahala APC ta mika mulki a ruwan sanyi idan ta sha kasa yadda Jonathan ya yi a 2015

  • Jagoran PDP a jihar Edo, Raymond Dokpesi ya ziyarci Benuwai, inda ya yi tir da gwamnatin APC
  • Raymond Dokpesi yace jam’iyyar APC ba za ta sallama mulki kamar yadda PDP ta yi a zaben 2015 ba
  • Cif Dokpesi ya na goyon bayan Atiku Abubakar ya karbe mulkin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP

Benue - Shugaban kamfanin DAAR Communications, kuma jigo a PDP, Raymond Dokpesi, yace babu tabbacin APC za ta mika mulki idan ta fadi zabe.

Jaridar Vanguard ta rahoto Cif Raymond Dokpesi yana cewa ba dole ba ne jam’iyyar APC ta yi irin abin da Goodluck Jonathan ya yi da ya sha kashi a 2015.

Raymond Dokpesi yace dole ne mutanen Najeriya su shirya karbe mulki daga hannun gwamnatin APC domin shawo kan matsalolin da suka addabi kasar nan.

Kara karanta wannan

A je a dawo mu na tare da Atiku, Tauraron ‘Dan wasan fim ya kunyata magoya-bayan Tinubu

‘Dan siyasar ya yi kira ga mutane da su zabi nagari wanda zai iya magance matsalar tsaro, kuma bai da tsanani da zafin ra’ayin addini da zai raba kan mutane.

Da yake jawabi a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba, 2021, Dokpesi ya koka cewa ana fama da matsalar rashin hadin-kai da rigingimun addini da kabilanci.

Jonathan
Buhari da Jonathan Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin da Raymond Dokpesi ya fada a Benuwai

“Kasar mu ta cika duk wasu shika-shikan gazawa. Gwamnatin APC ta gagara kare kasar nan da tattalin arzikinta daga sukurkucewa.” - Raymond Dokpesi.
“Matasanmu ba su da aikin yi. Lokacin da gwamnatin APC ta ke cewa za ta kawo canji, da dama sun bi su, sun dauka gaskiya aka yi masu alkawari.”
“Wasu daga cikinmu sun san ba za su iya rike kasar ba, mun san za su kashe tattalin arziki.”

Kara karanta wannan

2023: Duk ‘Dan shekara 60 ya hakura da neman mulki – CNYF ta ba Atiku, Tinubu jan-kati

“Yanzu da 2023 ta dumfaro, ba za mu cigaba da tafiya a haka ba. Hasashenmu ya nuna mafi yawan mutane na so PDP ta karbe mulki a hannun APC.”

Atiku Abubakar ake bukata

Reuben Abati ya rahoto Dokpesi yana cewa duk da kukan ‘yan Najeriya, ta tabbata APC ba za ta mika mulki cikin sauki yadda Goodluck Jonathan ya yi a 2015 ba.

“Shiyasa mu ke bukatar mu zauna, mu sake tunani. Mu na bukatar mutum irin Alhaji Atiku Abubakar ya ceci kasar nan.” – Raymond Dokpesi.

Ba na tare da Tinubu - Mr. Ibu

An ji cewa ‘Dan wasan kwaikwayon nan, John Ikechukwu Okafo watau Mr. Ibu yace ba ya tare da Bola Tinubu, jarumin yace Atiku ne ‘Dan takararsa a zaben 2023.

Da yake jawabi a Instagram, John Ikechukwu Okafo yace Atiku uba yake a wurinsa don haka ba zai ci amanar shi, ya kama layin Bola Tinubu na jam'iyyar APC ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel