Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ya gayyaci EFCC ta binciki kudin gina sakatariya da aka sace

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ya gayyaci EFCC ta binciki kudin gina sakatariya da aka sace

  • Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Okwesileze Nwodo yace an sace kudin da ya bari a asusun PDP
  • Dr. Okwesileze Nwodo yace kafin ya bar kujerarsa, PDP ta na da sama da Naira biliyan 11 a banki
  • Wadannan kudi da aka tara da sunan gina babbar sakatariya sun bace, kuma ba a gina ofishin ba

Abuja - Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Okwesileze Nwodo yace kudin da ya damkawa magajinsa domin gina sakatariyar jam’iyya sun bace.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Dr. Okwesileze Nwodo yana cewa Naira biliyan 11.8 da aka ware da nufin ginawa jam’iyyar PDP babban ofishi sun yi dabo.

Okwesileze Nwodo ya yi wannan bayani ne da yake gabatar da takarda a game da yadda ake tafiyar da jam’iyyar a wajen wani taro da aka shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

Karyar takunkumi Gwamnati ke yi, Sanatoci sun gano ana daukar yaran manya aiki a boye

Tsohon shugaban na PDP ya yi kira ga hukumomin yaki da rashin gaskiya su yi bincike, a hukunta wadanda suka saci kudi a asusun jam’iyyar adawar.

Okwesileze Nwodo yace abubuwa sun lalace

Dr. Nwodo ya koka, yace babu amana da gaskiya wajen yadda ake rike kudin jam’iyya a Najeriya.

Jam’iyyar PDP
Sakatariyar PDP da aka yi watsi da aikin Hoto: www.pressreader.com
Asali: UGC

“Babu gaskiya da keke-da-keke wajen rike dukiyar jam’iyya a yanzu. Na mika N11bn da N800m a asusun banki a lokacin da na bar kujerar shugaban jam’iyya bayan watanni bakwai.”
“Ban san me aka yi da wannan kudin ba. An tara miliyoyi domin a karasa ginin hedikwatar mu na kasa; babu labarin inda aka kai wadannan kudin, ba a iya karasa aikin gina ofishin ba.”
“A yau ba mu da asusun jam’iyya. Dole a koma lokacin da ake sa ido sosai kan kudin jam’iyya. Sai an karfafa sashen binciken kudi na cikin gida, shugabanni su dafa masu.” - Okwesileze Nwodo.

Kara karanta wannan

EFCC: Ma’aikacin banki ya tona yadda tsohon gwamna da SGG suka 'ci' N1.5bn a 2015

A kira EFCC - Nwodo

Jaridar Sun tace Nwodo ya bada shawarar a kira jami’an EFCC su yi bincike da nufin a hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen taba dukiyar jam’iyya.

“Ya wajaba a sa doka mai tsauri ga wadanda suka wawuri dukiyar jam’iyya. Ina bada shawarar mu gayyaci EFCC, su hukunta shugabanni da wadanda suka ci kudi, shi ne mafita.”

ICPC ta dafe Shehi a Kano

A jiya aka ji cewa hukumar ICPC ta na zargin shugaban karamar hukumar Fagge, Ibrahim Muhammad Abdullahi ya karkatar da harajin da aka tara.

Alkali ya bada belin Shugaban karamar hukumar ta Fagge da aka tuhuma a kan N500, 000. An daga shari'a, sai watan Junairun 2021 za a sake zama a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel