Tambuwal ya bayyana wanda ‘Yan Najeriya suke bukata ya zama Shugaban kasa a 2023

Tambuwal ya bayyana wanda ‘Yan Najeriya suke bukata ya zama Shugaban kasa a 2023

  • Gwamnan jihar Sokoto ya gabatar da jawabi a wajen wani taron shari’a da aka shirya a garin Abuja
  • Aminu Waziri Tambuwal ya ba mutane shawara game da wanda ya kamata a zaba a zaben 2023
  • Rt. Hon. Tambuwal ya gargadi mutane a kan zaben mutum kurum saboda addini, kabila ko yankinsa

Abuja - Mai girma gwamnan jihar Sokoto, ya yi kira ga jama’a da su guji zaben wanda zai rika daukar wasu bangare na kasar nan kamar ribatattun yaki.

Jaridar The Cable tace Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron shari’a da aka shirya a babban birnin tarayya Abuja.

Mai girma Aminu Waziri Tambuwal yace idan an zo zaben 2023, ya kamata mutane su zabi shugaban da zai iya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari

“Najeriya tana bukatar shugaban kasa wanda ya san kan abubuwa da yawa, wanda yake da abokai a kowane yanki na kasar nan.”
“Ana bukatar shugaban kasa wanda kan sa ya waye ne, ba kifin rijiya ko wanda iyakar sa wani bangare ba.” – Aminu Tambuwal.
Tambuwal
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Hoto: @BBCNewsHausa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta rahoto shugaban gwamnonin na jam'iyyar PDP yana cewa hanyar da za a yaki rashin gaskiya ita ce kawo dokokin da ba za a iya yi wa dabara ba.

Ya za a magance matsalar tsaro?

“Mu na bukatar shugaba mai gaskiya, wanda ya fahimci cewa yadda za a yaki rashin gaskiya ita ce a kafa dokoki masu karfi da sun fi karfin a kewaye su.”
“Najeriya na bukatar shugaban da ya san halin da ake ciki a yau, ya fahimci inda dosa wajen shawo kan matsalolin al’umma ta hanyar amfani da fasaha.” - Tambuwal.

Kara karanta wannan

Shugaban Najeriya Buhari zai ba Gwamnoni 36 bashin Naira Biliyan 650 da za a karba a 2051

Tambuwal ya kara da cewa ana bukatar shugaba mai tausayi, wanda ya damu da halin da talaka da mabukata su ke ciki, wanda al’umma za su iya dogara da shi.

An rahoto gwamnan na Sokoto yana cewa ana bukatar wanda zai rike jama’a ba tare da son-rai ba, wanda ba zai dauki wasu tamkar bayin da aka ribata a yaki ba.

Sabani tsakanin gwamnonin APC

A yau aka ji cewa dokar zabe ta raba kan gwamnonin jihohin APC, har ta kai an yi cacar baki a wajen taron Jam’iyya da aka gudanar a gidan gwamnan jihar Kebbi.

‘Yan majalisa na so a canza dokar zabe, abin da bai kwantawa wasu Gwamnoni a rai ba. Hakan ya jawo takaddama tsakanin Abdullahi Sule da Gwamna Yahaya Bello.

Asali: Legit.ng

Online view pixel