Mun ba Shekarau fam kyauta, amma babu abin da ya taba bamu sai N100, 000 - APC Kano

Mun ba Shekarau fam kyauta, amma babu abin da ya taba bamu sai N100, 000 - APC Kano

  • Abdullahi Abbas wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano ya fede Ibrahim Shekarau
  • Alhaji Abdullahi Abbas yace babu abinda tsohon gwamnan ya iya tsinanawa jam’iyyar APC tun 2019
  • ‘Dan Sarki ya zargi Sanata Shekarau da cin amanar Gwamna Abdullahi Ganduje da watsi da jam’iyya

Kano - Shugaban jam’iyyar APC ta reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya yi karin haske a kan abubuwan da suke faruwa a siyasa da gwamnatin Kano.

A wata gajerar hira da aka yi da Alhaji Abdullahi Abbas, ya zargi Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau da son kai da watsi da jam’iyyar APC.

Jaridar Sahelian Times ta kawo rahoto game da yadda wannan hira ta kasance, inda shugaban na APC ya yi wa Shekarau kaca-kaca, har da yi masa gori.

Read also

'Dan majalisa ya sake komawa PDP bayan makwanni kaɗan da komawarsa APC, ya bayyana dalili

A cewar Abdullahi Abbas, ‘yanuwa da abokan Ibrahim Shekarau kadai suke amfana da shi tun da APC ta yi masa hanya ya samu kujerar Sanata a bagas.

Shugaban APC mai mulki a Kano yace tun da Shekarau ya zama Sanata babu abinda jam’iyya ta samu a hannunsa sai N100, 000 a lokacin wani bikin sallah.

Jam'iyyar APC ta mutum uku ce?

Abbas yana kare kan shi ne daga sukar cewa yace jam’iyyar APC ta mutane uku ce a jihar Kano, inda yace irinsu Shekarau ba su yi wa APC hidima ta siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC a Kano
Jagororin APC a Kano Hoto: @faizualfindikii
Source: Facebook

‘Dan siyasar da aka fi sani da ‘Dan Sarki, jikan Sarki a Kano, yace ya fadi hakan ne domin gwamna da mai dakinsa da shi kansa ne suke hidima da jam’iyyar APC.

Babu abin da Shekarau ya tsinanawa APC?

Read also

Gwamnan PDP ya ba Buhari shawara ya yi watsi da kudirin da Majalisa za ta kawo gabansa

A wannan hira, Abbas ya zargi tsohon gwamnan da rashin tabuka kirki a zaben 2019, yace Shekarau bai iya kawowa APC akwatinsa a unguwar Giginwu ba.

Yanzu da ya zama ‘dan majalisar dattawa, Sanata Ibrahim yana yawo zuwa Dubai, Tanzaniya, yana watayawa abinsa, har yana gani ko babu tabarau, inji Abbas.

Shugaban na APC ya musanya zargin cewa ba a tafiya da su Shekarau, yace idan za ayi taro yana kiransu a waya, amma sai a fada masa ya bar kasar, yana ketare.

Dama tun can Abbas yace sun san tsohon Ministan ilmin zai rabu da gwamna Abdullahi Ganduje, kamar yadda ya ‘yaudari’ Muhammadu Buhari bayan zaben 2003.

Majalisar shurar Sardaunan Kano

Dazu ne muke samun labarin cewa, 'yan siyasa biyu da suka dawo tsagin Ibrahim Shekarau sun karbi takardun mukamai daga bangaren tsohon gwamnan na Kano.

Shekarau ya nada tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Hafifzu Abubakar da tsohon kakakin majalisar Kano, Hon. Gambo Sallau a matsayin 'yan majalisar shawara.

Read also

Yadda tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya canza gidan siyasa sau 6 a shekara 7

Source: Legit.ng

Online view pixel