'Dan majalisa ya sake komawa PDP bayan makwanni kaɗan da komawarsa APC, ya bayyana dalili

'Dan majalisa ya sake komawa PDP bayan makwanni kaɗan da komawarsa APC, ya bayyana dalili

  • Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ekwusigi a majalisar jihar Anambra, Onyebuchi Offor ya kara komawa jam’iyyar PDP
  • A watan Satumban da ya gabata ne Offor ya koma APC har yana cewa lokaci ya yi da zai shiga jam’iyya mai mulki don ya ji yadda ake ji
  • Sai dai dan majalisar ya bayyana kara komawarsa PDP ranar Alhamis inda ya ce hakan ya biyo bayan shawarwarin da ya yi da mutanensa

Jihar Anambra - 'Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ekwusigo a majalisar dokokin jihar Anambra, Onyebuchi Offor ya kara komawa jam’iyyar PDP, The Cable ta ruwaito.

Offor ya koma jam’iyyar APC daga PDP a watan Satumban da ya gabata.

Dan majalisa ya sake komawa PDP bayan makwanni kaɗan da komawarsa APC
Dan majalisar Anambra ya sake komawa PDP bayan makwanni kaɗan da komawarsa APC. Hoto: The Cable
Source: Facebook

Read also

Gwamnan PDP ya ba Buhari shawara ya yi watsi da kudirin da Majalisa za ta kawo gabansa

Kamar yadda The Cable ta bayyana ya ce a lokacin, 'Lokaci ya yi da zan shiga jam’iyyar don mazabata ta ji yadda ake ji a cikin jam’iyya mai mulki.;

Dan majalisar ya bayyana kara komawarsa PDP a Awka ranar Alhamis. Ya ce ya yanke shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsakin mazabarsa.

Ya ce PDP ta fi APC

NAN ta ruwaito inda ya ke cewa:

“A watanni biyu da su ka gabata, na bayyana yadda na sauya sheka daga PDP zuwa APC a cikin wannan gidan. Na dandana jam’iyyar sannan na gane cewa PDP ta fi ta.
“Hakan ya sa nake so in sanar da gidan nan cewa zan koma jam’iyya ta ta PDP.”

Noble Igwe, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ogbaru I, ya yi wa Offor barka da komawa jam’iyyar inda ya ce:

“Da PDP ta samu nasarar cin zaben gwamna da Offor bai koma jam’iyyar APC ba. Komawarka babbar asara ce ga PDP din Anambra amma mu na maka barka da dawowa PDP don dama da ita ka dace.”

Read also

APC ta ja wa Marafa kunne da kakkausar murya, ta bayyani matakin da za ta dauka a kan shi

Uche Okafor, kakakin majalisar yayin jawabi a majalisar ya ce kowa ya na da damar komawa duk jam’iyyar da ya ga dama kuma ya na yi wa Offor fatan alheri.

A ranar 21 ga watan Satumba, ‘yan majalisu 4 ne su ka koma APC daga jam’iyyar APGA.

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Source: Legit.ng

Online view pixel