Gwamnan PDP ya ba Buhari shawara ya yi watsi da kudirin da Majalisa za ta kawo gabansa

Gwamnan PDP ya ba Buhari shawara ya yi watsi da kudirin da Majalisa za ta kawo gabansa

  • Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya soki kwaskwarimar da majalisa tayi wa dokar zabe
  • Samuel Ortom yace zai fi kyau a bar jam’iyyar siyasa ta tsaida ‘dan takararta duk yadda ta ga dama
  • A wata zantawa da ‘yan jarida, Ortom ya bayyana yadda Dr. Iyorchia Ayu ya zama shugaban PDP

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya maida kudirin gyara dokar zabe da za a kawo masa.

Daily Trust ta rahoto gwamna Samuel Ortom yana cewa ya kamata shugaban kasa ya maidawa ‘yan majalisa kudirinsu, domin a ba jam’iyyu dama.

Gwamnan ya na so jam’iyyu su rika fito da ‘yan takara duk yadda suka ga dama, akasin shirin majalisa na wajabta amfani da zaben kato-bayan-kato.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro sama da 100 a jihar Benuwai

Mista Ortom ya yi wannan roko lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin tarayya Abuja, a ranar Talata, 16 ga watan Nuwamba, 2021.

Dokar zabe ba za tayi aiki a haka ba - Ortom

A cewar Ortom, majalisa ba ta sa kishin kasa da take aiki kan wannan kudirin ba. Gwamnan na PDP ya kawo dalilan da za su hana dokar aiki da kyau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Benuwai
Shugaba Buhari da Ortom Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Gwamnan na Benuwai yace zai yi wahala jam’iyyu su rika fito da ‘dan takara ta hanyar zaben kato-bayan-kato domin ba su da arzikin shirya zabukan.

Baya ga haka, Ortom yace jam’iyyun da ke kasar nan ba su da ikon da za su sa ido ayi wannan zabe. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoton a jiya.

“Dokar ta kyale jam’iyyu su zabi hanyar da suke so su fito da ‘yan takararsu a zabe.” – Ortom.

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

Da yake kare matsayinsa, Samuel Ortom yace gwamnoni suna yakar dokar ne ba don su na da niyyar murde zabuka ba, yace za a iya murdiya duk a haka.

Har ila yau, Ortom ya bayyana yadda Dr. Iyorchia Ayu ya zama shugaban PDP, yace David Mark ne yace a bar Ayu ya rike jam’iyyar domin su din abokan juna ne.

Hafizu Abubakar ya raba jiha da Abdullahi Umar Ganduje

A jiya aka ji Farfesa Hafizu Abubakar ya bar tsagin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya hada-kai da kungiyar G7 da ke karkashin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.

Hafizu Abubakar ba bakon tanga-tangal ba ne a siyasa, ya shiga jam’iyyu barkatai. Daga shekarar 2014 zuwa yanzu, Farfesa ya shiga ya fita APC, PDP da kuma PRP

Asali: Legit.ng

Online view pixel