Kaduna za ta daina dogara da abin da za a samu daga asusun Tarayya - Gwamnatin El-Rufai

Kaduna za ta daina dogara da abin da za a samu daga asusun Tarayya - Gwamnatin El-Rufai

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta kama hanyar dogara da kudin shigan ta, ba tare da jiran kason FAAC ba
  • Kwamishinan kasafi, Muhammad Sani Dattijo ya shaidawa ‘yan majalisar dokokin jihar wannan
  • Kusan 30% na kasafin kudin jihar Kaduna ne kacal yake fitowa daga kason gwamnatin tarayya

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna tace ta na kokarin ganin ta samu duk kudin da ta ke bukata a kasafin shekara shekara daga abin da samu a cikin gida.

Jaridar Punch ta rahoto kwamishinan kasafi da tsare-tsare na Kaduna, Muhammad Sani Dattijo yana cewa za su bunkasa kudin shigan da su ke samu.

Malam Sani Dattijo ya bayyana wannan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin jihar Kaduna a cikin makon nan.

Kwamishinan yace idan aka cigaba da tafiya a haka, nan da wasu shekaru, duk abin da zai zo cikin asusun gwamnatin Kaduna bayan IGR zai zama nafila.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar kasar Amurka ta garkamawa Najeriya takunkumin sayen kayan yaki

'Yan majalisa sun bada gudumuwa

Jaridar Premium Times ta rahoto kwamishinan kasafin yana cewa majalisar dokoki ta bada gudumuwa wajen bunkasa kudin shigan da su ke samu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon hadimin na gwamna Nasir El-Rufai yace Kaduna za ta tashi daga jihar da ta dogara da gwamnatin tarayya zuwa wanda ta ke iya tsayuwa da kanta.

Gwamnatin El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai da Sani Dattijo Hoto: @Govkaduna
Asali: Facebook

Daga N13bn, kudin-shigar Kaduna ya koma N57bn

“A 2015 da gwamnatin nan ta zo, mafi yawan abin da muka taba samu shi ne N13bn a shekara, yanzu mun kai N57bn da taimakon majalisa.” – Dattijo.
“Gwamnatin jiha ta dogara ne da 31% kacal na kasafin kudinta daga asusun tarayya, yayin da wasu jihohin sun dogara da tarayya wajen samun 70-80%.”

Nan gaba duk wasu ayyukan more rayuwa da dawainiyar da gwamnatin Kaduna za ta yi, za ta aiwatar ne daga asusun tara kudin shigan harajinta na IGR.

Kara karanta wannan

Gombe: Gwamna Inuwa Yahaya ya haramta wa makiyaya shiga jihar

Gwamnatin Buhari za ta ba jihohi aron kudi

A jiya aka ji gwamnatin Najeriya za ta ba Gwamnoni 36 bashin Naira Biliyan 650. Wannan bashi zai taimakawa jihohin wajen biyan bashin da aka ba su a baya.

Kowace Jiha za ta karbi aron Naira biliyan 18.22 da za a biya nan da shekaru 30. Wannan bashi zai taimakawa jihohi su sauke nauyin bashin da ke kan wuyansu

Asali: Legit.ng

Online view pixel