Wata Sabuwa: Jam'iyyar PDP ta kasa ta dage babban gangamin taronta na Arewa

Wata Sabuwa: Jam'iyyar PDP ta kasa ta dage babban gangamin taronta na Arewa

  • Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ta dakatar da babban gangamin taron ta na yankin arewa maso yamma da take shirin gudanarwa
  • Sakataren shirye shirye na kwamitin NWC ne ya sanar da haka, yace sun ɗauki wannan matakin ne domin guje wa abinda ka iya zuwa ya dawo
  • Ya roki masu ruwa da tsaki, shugabanni da mambobin PDP a yakin su yi hakuri, za'a sanar da sabuwar rana ba da jima wa ba

Abuja - Kwamitin gudanar da ayyuka (NWC) na jam'iƴyar PDP ta ƙasa ya sanar da ɗage gangamin taron jam'iyya a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Punch ta rahoto cewa kafin wannan matakin PDP ta shirya gudanar da gangamin taronta a arewa ta yamma ranar 20 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: 'Yan sanda sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC a Abuja

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren shirye-shirye na kwamitin NWC, Austin Akobundu, ya fitar ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja.

Jam'iyyar PDP
Wata Sabuwa: Jam'iyyar PDP ta kasa ta dage babban gangamin taronta na Arewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace kwamitin NWC ya ɗauko wannan matakin dage baban taron ne bayan neman shawarwari da tuntuban masu ruwa da tsaki.

Meyasa PDP ta dauki matakin dage taron?

A sanarwan da sakataren shirye shiryen ya fitar, yace:

"Mun ɗauki wannan matakin ne bayan hasashen abinda ka iya zuwa ya dawo ko kuma abinda ka iya faruwa da zai zama cikas wajen gudanar da babban taron."
"Kwamitin NWC na rokon jiga-jigan masu ruwa da tsaki, shugabannin jam'iyya da mambobin jam'iyya a yankin arewa maso yamma su san da wannan matakin."
"Kwamitin mu zai sanar da sabuwar ranar da za'a gudanar da wannan babban taron da zaran an cimma matsaya."

Kara karanta wannan

Abu daya ya rage mu kawo karshen yan ta'adda da yan bindiga a Najeriya, Hafsan Soji

PDP ta samu nasara a taron ta na ƙasa

Idan baku manta ba a baya dai jam'iyyar PDP ta gudanar da babban gangamin taron ta na kasa cikin nasara tare da zaɓo sabbin shugabanninta a matakin kasa.

Ba'a yi tsammanin PDP zata kammala taron ba tare da samun matsala ba, kasancewar rikicin da take fama da shi, kamar yadda PM News ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Game da Barazanar ASUU

Mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya yi kira ga shugaba Buhari ya cika alkawarin da gwamnatinsa ta yi wa ASUU.

Basaraken yace a musulunci, Allah ba ya ɗaukar Alkawari ya ki cikawa, kuma yana da kyau mutum ya zama mai cika alkawari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel