Kwanaki da lashe zabe, an shigar da Soludo a kotu, ana neman hana shi zama Gwamnan Anambra

Kwanaki da lashe zabe, an shigar da Soludo a kotu, ana neman hana shi zama Gwamnan Anambra

  • Adindu Valentine da Egwudike Chukwuebuka su na tuhumar nasarar Charles Soludo a Anambra
  • Ana zargin Farfesa Charles Soludo a kotu cewa ya yi karya wajen cike fam din shiga takarar gwamna
  • A dalilin wannan aka shigar da kara, ana neman a ruguza nasarar da ya samu a zaben Anambra

Abuja - The Nation tace an shigar da kara a kotun tarayya na Abuja, ana neman a kalubalanci nasarar Charles Soludo da Onyeka Ibezim a zaben Anambra.

Adindu Valentine da Egwudike Chukwuebuka su na ikirarin cewa Farfesa Charles Soludo ya gabatarwa hukumar INEC da bayanan karya kafin shiga zaben.

Masu karar sun ce Charles Soludo wanda shi ne ya yi nasara a jam’iyyar APGA bai cancanci ya rike kujerar gwamna ba a dalilin karyar da ya yi wajen cike fam.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan PDP ya amince da shan kaye, ya taya Soludo murna

A wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/711/2021 da Valentine da Chukwuebuka suka shigar, sun ce Soludo ya nuna yana takarar kujerar ‘dan majalisar Aguata ne.

A maimakon fam din shiga takarar tsohon gwamnan na CBN ya nuna zai nemi kujerar gwamna, sai ya cika cewa yana neman zama ‘dan majalisar yankin Aguata.

Sabon Gwamnan Anambra
Farfesa Charles Soludo Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me lauyoyi suka fadawa kotu?

Lauyoyin da suka tsayawa masu karar O. Ijeri da Kelvin Okoko sun ce wannan danyen aiki da Soludo ya yi, ya nuna ya ba INEC bayanan da ba gaskiya ba ne.

A dalilin wannan, Ijeri da Okoko suka ce zababben gwamnan ya saba doka, kuma a soke nasararsa. INEC tace ba za ta bata lokacin kare kanta a kotu ba.

Wadanda suka kai karar su na tuhumar hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC, jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, Soludo da Dr. Ibezim.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Manya-manyan ‘Yan siyasa 5 da suka fi kowa cin ribar nasarar APGA

An sa ranar da APGA za ta san makomarta

Jaridar Punch tace Alkali mai shari’a Taiwo Taiwo, ya zabi 30 ga watan Nuwamba, 2021, a matsayin ranar da ‘dan takarar da ya lashe zaben zai san makomarsa.

Lauyan da APGA da Farfesa Soludo suka dauko, Onyechi Ikpeazu (SAN), ya nemi ayi fatali da karar domin ba ta da wata madogara, ya kafa hujja da dokar zabe.

Rotimi Akeredolu ya ba 'dan sa mukami

A jiya ne gwamna Rotimi Akeredolu ya zabi 'dansa, Babajide a matsayin DG na hukumar PPIMU. Ba kasafai dai aka saba jin cewa Gwamna ya ba 'dansa mukami ba.

Rotimi Akeredolu SAN ya taba bugun kirjin cewa zai ba ‘dansa mukami, kuma dole a zauna lafiya. A wancan lokaci mutane sun yi tunanin ba'a gwamnan yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel