Gwamnan Ondo ya nada ‘Dan cikinsa a cikin Gwamnatin jiha, ya ba shi Darekta Janar

Gwamnan Ondo ya nada ‘Dan cikinsa a cikin Gwamnatin jiha, ya ba shi Darekta Janar

  • Mista Babajide Akeredolu ya shiga cikin mukarraban gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu SAN
  • Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana wannan ne a wani jawabi da kwamishinansa ya fitar a jiya
  • Sanarwar tace Babajide Akeredolu zai jagoranci hukumar PPIMU da ke lura da kwangiloli a jihar

Ondo - Mai girma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya yi abin da ba a saba ji ba, yayin da ya zabi ‘dan cikinsa a cikin wadanda zai ba mukamai.

Gwamna Rotimi Akeredolu ya nada Babajide Akeredolu a matsayin Darekta-Janar na hukumar PPIMU mai sa ido a kan aiwatar da kwangiloli a Ondo.

Daily Trust tace PPIMU ce ta ke da alhakin lura da yadda ayyuka suke gudana a gwamnatin Ondo. Wani rahoton yace Babajide ya dade a gwamnatin mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Abubuwa 17 da ya kamata ku sani a rahoton da kwamitin Endsars ya gabatar

An bada sanarwar ba Babajide Akeredolu mukami a lokacin da gwamna ya fitar da jerin wadanda yake so ya nada a matsayin sababbin kwamishinoninsa.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan al’umma, Donald Ojogo, ya bada wannan sanarwa a jawabin da ya fitar a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2021.

Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, ya zabi mutane 14 da zai ba kujerar kwamishina, da wasu bakwai a matsayin hadimansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Ondo
Gwamna da Babajide Akeredolu Hoto: orientaltimes.com
Asali: UGC

Sauran wadanda za a ba mukami a Ondo

Kwamishinonin su ne Bamidele Olateju, Otunba Adefarati Gboyega, Rt Hon Olotu Fatai, Dr. Julianah Oshadahun, Otunba Dele Ologun da Sunday Kunle.

Sai Razaq Obe, Dr. Banji Ajaka, Fasto Emmanuel Igbasan, Yetunde Adeyanju, Femi Agagu, Hon. Akinlosotu, Olayato Aribo da kuma Hon Omolola Fagbemi.

Sababbin hadiman gwamna Akeredolu

Wadanda za su zama masu bada shawara sun hada da Dr. Victor Ategbole, Dr. Wunmi Egbayelo Ilawole, Barista Tobi Ogunleye Felix, da Olamide Falana.

Kara karanta wannan

Harin ISWAP a Borno: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Janar din aka kashe

Sai Dr. Ajibayo Adeyeye, Olamide Falana, Dr. Francis Adedayo Faduyile da Oyeniyi Oseni.

PPIMU ce ta ke da alhakin lura da yadda ayyuka ke gudana. Akeredolu ya taba cewa zai iya nada 'dansa shugaban ma’aikatar fadarsa, kuma dole a zauna lafiya.

Muhammadu Buhari ya yabi Goodluck Jonahan

A jiya da yamma ne aka ji cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasar Najeriya murnar cika shekaru 64 a duniya.

Muhammadu Buhari ya bayyana yadda Goodluck Jonahan ya bambanta da sauran mutane wajen mayar da hankalinsa kan shugabanci da jagorancin al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel