Kasar Amurka ta yaba da sakamakon zaben jihar Anambra, ta nuna ba a tafka magudi ba

Kasar Amurka ta yaba da sakamakon zaben jihar Anambra, ta nuna ba a tafka magudi ba

  • Gwamnatin kasar Amurka ta yaba da yadda INEC ta gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra.
  • Ofishin jikadancin Amurka yace sakamakon zaben ya nuna abin da al’ummar Anambra suka zaba.
  • Kasar Amurka tayi kira ga hukumar INEC ta inganta aikinta kafin zabukan da za ayi a Osun da Ekiti.

Abuja - Gwamnatin kasar Amurka ta jinjinawa zaben sabon gwamnan da aka gudanar a jihar Anambra. Wannan karo jakadancin ya yabi INEC.

Amurka ta bayyana wannan ne a wani jawabi da ta fitar ta bakin ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, 2021.

Jaridar Vanguard tace ofishin jadakancin na Amurka ya fitar da jawabi a jiya mai taken: “Jawabi a kan zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar.”

Jawabin ofishin jakadancin yace sakamakon zaben ya nuna ra’ayin mutanen jihar Anambra.

Read also

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

Punch ta rahoto gwamnatin Amurkan tana yabawa INEC da jami’an tsaro da duk kungoyoyin da suka tsaya ka’in da na’in wajen ganin an yi zaben kwarai.

Kasar Amurka
Ana zabe a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin da Ofishin jakadancin Amurka ya fitar

“Gwamnatin kasar Amurka tana taya mutanen jihar Anambra murnar gudanar da zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba a cikin zaman lafiya.”
“Sakamakon zaben da aka fitar, ya tabbatar da ra’ayin al’umma.” – Ofishin jakadancin Amurka.
“Mun lura da kalubalen da hukumar zabe na INEC da jami’an tsaro suka fuskanta wajen zaben, kuma muna jinjinawa kokarinsu na yin zabe mai nagarta.”
“Mun kuma yaba da kokarin da kungiyoyi masu zaman kansu suka yi tukuru wajen wayar da kan masu kada kuri’a da tabbatar da an yi zabe mai nagarta.”
“Muna sa ran a a cigaba da samun cigaba a harkar zabe a kasar nan yayin da ake shirin zaben gwamnoni a Osun da Ekiti kafin babban zabe na 2023.”

Read also

Rahoto: INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zabe a wasu rumfuna a zaben Anambra

Siyasa babu gaba a Anambra

A jiya aka ji ‘dan takarar jam'iyyar YPP, Sanata Ifeanyi Uba ya kira Gwamna mai-jiran gado, Charles Soludo bayan ya sha kashi a zaben da aka gudanar.

Ifeanyi Uba ya rungumi kaddara, ya hakura da sakamakon zaben na jihar Anambra, ya taya Farfesa Charles Soludo nasara, duk da yace an samu cikas.

Source: Legit.ng

Online view pixel