Matasa sun fara nuna ba za su goyi bayan Atiku, Kwankwaso da duk wani tsohon 'Dan takara ba

Matasa sun fara nuna ba za su goyi bayan Atiku, Kwankwaso da duk wani tsohon 'Dan takara ba

  • Shugaban Arewa Youth Consultative Forum ya yi magana a game da zaben shugaban kasa na 2023.
  • Kungiyar AYCF tace ba za ta goyi bayan duk wani ‘dan takarar da ya zarce shekara 60 da haihuwa ba.
  • Yerima Shettima yace ba su tsaida ‘dan takara ba, amma suna so a canza tsarin shugabancin Najeriya.

Kaduna - Arewa Youth Consultative Forum tace ‘ya ‘yanta ba za su goyi bayan duk wani ‘dan takarar shugaban kasa da shekarunsa suka wuce 60 ba.

Kungiyar matasan Arewa ta bayyana wannan ne a lokacin da shugabansu na kasa watau Yerima Shettima ya ke zantawa da manema labarai a garin Kaduna.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021, inda aka ji Ambasada Yerima Shettima yana magana a game da zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna

Yerima Shettima yace kungiyarsu ta AYCF za ta goyi bayan ‘dan takarar da yake da jini a jikinsa.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Arewa Youth Consultative Forum tace har yanzu ba ta yanke shawarar ‘dan siyasar da za ta goyawa baya a zaben 2023 ba.

Akwai gyara kafin 2023 - Arewa Youth Consultative Forum

Ambasada Shettima yace akwai wasu abubuwa da dama da AYCF za ta lura da su, kafin ta tsaida zabinta, amma yace akwai bukatar ayi wa tsarin kasa gyara.

Tinubu da Buhari
Tinubu da Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

“Ina cikin masu kiran a sake yi wa Najeriya fasali. Idan muka cigaba da tattara karfin iko a bangare guda, za muyi ta samun na banza a mulki.” – Shettima.

Shekarun 'yan takarar 2023

Mafi yawan wadanda ake hasashen za su yi takarar shugaban kasa a zaben 2023 sun haura shekara 60. Sai dai babu wanda yace yana neman mulkin.

Kara karanta wannan

Tsohon Tauraron Barcelona zai dawo kungiyar a matsayin koci bayan sallamar Koeman

Idan har Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta tafi da wannan ra’ayin, akwai yiwuwar ta raba jiha da irinsu Atiku Abubakar da Asiwaju Bola Tinubu.

Wadannan manyan ‘yan siyasa da ake ganin watakila su nemi takara duk za su zarce shekara 70 a 2023. A bana ne Rabiu Musa Kwankwaso ya cika shekara 65.

Bukola Saraki zai cika shekara 60 a shekarar 2023, yayin da irinsu gwamna Yahaya Bello da Aminu Waziri Tambuwal za su ji dadin wannan ka'ida na AYCF.

Baraka a jam'iyyar PDP

A makon da ya gabata ne aka ji sabani ya shiga cikin jam'iyyar PDP na reshen jhar Ondo bayan tsohon Gwamna, Dr. Segun Mimimko da mutanensa sun shigo.

Wasu daga cikin kusoshin PDP ba su ji dadin sauya-shekar tsohon gwamnan na Ondo ba. APC tace da dawowar Segun Mimiko da zamansa a ZLP duk daya ne.

Kara karanta wannan

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel