Tsohon Tauraron Barcelona zai dawo kungiyar a matsayin koci bayan sallamar Koeman

Tsohon Tauraron Barcelona zai dawo kungiyar a matsayin koci bayan sallamar Koeman

  • Al Sadd ta tabbatar da cewa Xavi Hernandez ya tashi daga Kungiyar bayan Barcelona ta biya fam €5m.
  • Ana sa ran Barcelona za ta nada Xavi Hernandez a matsayin kocin da zai maye gurbin Ronald Koeman.
  • Tsohon ‘dan wasan zai bar kungiyar da ya bari shekaru shida da suka wuce, bayan ya yi shekara 17.

Qatar - Al Sadd ta bada sanarwar cewa Xavi Hernandez ya tashi a ranar Juma’a, 5 ga watan Nuwamba, 2021. Jaridar AS ta fitar da wannan rahoton.

Hakan ya kara tabbatar da rade-radin cewa Xavi Hernandez zai koma kungiyar Barcelona. Hakan na zuwa ne bayan an kori Ronald Koeman daga aikinsa.

Kungiyar Al Sadd tace Barcelona ta biya fam miliyan €5 domin ta dauke mai horas da ‘yan wasan.

Kara karanta wannan

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

AS tace Al Sadd ta fitar da jawabi tace Xavi ya amince ya koma Barcelona bayan biyan kudin da ke kansa, kamar yadda aka yi yarjejeniya a kwantiraginsa.

Kocin mai shekara 41 ya shafe shekara shida yana horas da kungiyar ta kasar Qatar. Watakila nan ‘yan awanni a bada sanarwar zuwansa a filin Camp Nou.

Barcelona
Xavi da yake wasa a Barcelona Hoto: news.sky.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a fitar da sanarwa ba tukuna?

Kawo yanzu dai babu sanarwar da ta fito daga Barcelona a game da nada tsohon ‘dan wasan tsakiyan a matsayin babban mai horas da ‘yan kwallonta.

Da aka tambayi kocin da aka nada na wucin gadi kafin wasan Celta, ya sake jaddada cewa har yanzu ba a kai ga nada sabon mai horas da ‘yan wasa ba.

Goal.com ta kawo rahoto cewa tsohon ‘dan wasan na kasar Sifen zai karbi aikin horas da kungiyar Barcelona daga hannun kocin rikon kwarya Barjuan.

Kara karanta wannan

Habasha: 'Yan tawaye sun kewaye Addis Ababa, firaminista ya ce kowa ya dauki makami

Amma Sergi Barjuan ne zai jagoranci kungiyar ta Sifen a wasan Celta Vigo. Ana sa ran Xavi zai karbi ragamar kungiyar a wasansu na mai zafi da Espanyol.

Al-Sadd ta wallafa bidiyo inda aka ga Xavi yana hawaye yayin da yake kukan ban-kwana da kungiyar. ‘Yan wasansa sun yi masa fatan alheri a kasar Sifen.

Sergio Ramos zai bar Faransa?

Kungiyar Paris Saint-Germain ta musanya rahotannin da suke yawo cewa tana tunanin katse kwantiragin Sergio Ramos, tun kafin ya kai ga fara buga wasa.

arektan wasannin na kungiyar PSG, Leonardo Araujo yace babu gaskiya a jita-jitar da ke yawo. Leonardo yace dama can sun san da 'dan wasan yana da rauni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel