PDP ta fara darewa bayan Tambuwal da Gwamnoni sun yi babban kamu, sun dawo da Mimiko

PDP ta fara darewa bayan Tambuwal da Gwamnoni sun yi babban kamu, sun dawo da Mimiko

  • Kwanakin baya wasu manyan gwamnonin PDP suka sa Dr. Olusegun Mimiko ya bar jam’iyyar ZLP.
  • Tsohon gwamnan Ondo wanda aka fi sani da Iroko, zai sauya-sheka zuwa PDP da magoya-bayansa.
  • Sauya-shekar babban ‘dan siyasar ta jawo sabani a gidan PDP, har wasu na shirin shigar da kara a kotu.

Ondo - Shigowar Dr. Olusegun Mimiko cikin jam’iyyar PDP ya jawo wasu matsaloli a reshen jihar Ondo. Jaridar Punch ta bayyana wannan a wani rahoto.

Shigowar Olusegun Mimiko cikin PDP bayan gwamnonin adawa a karkashin jagorancin Aminu Tambuwal ya jawo an nakasa jam’iyyar ZLP a Najeriya.

Labarin sauya-shekar tsohon gwamnan ya fara raba kan PDP mai adawa a jihar Ondo. Wasu suna murna da dawowarsa, wasu kuma suna matukar shakkarsa.

Kara karanta wannan

An gano yadda Wike, Tambuwal da Gwamnoni suka raba mukaman PDP a tsakaninsu

Rahoton yace wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP suna ganin cewa Mimiko bai da tabbas, a ko yaushe zai iya sauya sheka kamar yadda ya saba yi a da.

Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa, Dr Eddy Olafeso, ya ji dadin jin cewa Dr Olusegun Mimiko ya dawo PDP, yace zai taimakawa jam’iyyar a Ondo.

Mimiko
Segun Mimiko
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bode Obanla yana adawa da Mimiko

Jiga-jigan PDP a Ondo irinsu Bode Obanla suna da ra’ayi dabam, suna ganin bai dace a ba tsohon gwamna wani mukami daga zuwansa jam’iyyar hamayyar ba.

Bode Obanla yana ikirarin wannan shi ne abin da dokar PDP tace, har yana barazanar kai jam’iyyarsa kotu a kan sauya-shekar fitaccen ‘dan siyasar.

“Nayi farin ciki domin doka ta bani dama in kai Mimiko kotu da yake shirin shigowa PDP. Na fadawa Lauya na ya fara shiri tun yanzu.” – Bode Obanla.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnonin PDP suka nunawa Atiku da Saraki iko a zaben Shugabannin Jam’iyya

Aikin banza, an mari jaki - APC

Shi kuma shugaban APC na jihar Ondo, Ade Adetimehin cewa ya yi dawowar Mimiko cikin PDP ba zai canza komai ba, yace jam’iyyarsu ta riga tayi karfi.

Hadimin tsohon gwamnan, John-Paul Akinduro, ya yi wani jawabi mai kamar martani, inda yace mai gidansa zai taimaka wajen kifar da APC a zaben 2023.

Wanene 'Dan takarar APC a zaben Anambra?

Yayin da ake shirin zaben Anambra, mun kawo maku abubuwan da ya kamata a sani game da Sanata Andy Uba, wanda na hannun daman Obasanjo ne.

Sau biyu ana soke zaben da Andy Uba ya yi nasara, kafin ya lashe kujerar Sanata a 2019

Asali: Legit.ng

Online view pixel