Da duminsa: Soludo ya lashe karamar hukuma ta 8, ya na jagoranci da tazarar kuri'u 36K

Da duminsa: Soludo ya lashe karamar hukuma ta 8, ya na jagoranci da tazarar kuri'u 36K

  • Dan takarar jam'iyya mai mulkin jihar Anambra, Charles Soludo, ya sake lashe zabe a karamar hukumar ta takwas
  • A halin yanzu ya na da kuri'u 4,826 a karamar hukumar Orumba ta arewa inda ya samu jimillar kuri'u 60,988
  • Soludo ya yi fintinkau inda ya ke sahun gaba da tazarar kuri'u 36,016 yayin da Valentine Ozigbo na PDP ke take masa baya

Anambra - Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance ta sake lashe karamar hukumar Orumba ta arewa a zaben gwamnan jihar Anambra da ke gudana, Daily Trust ta ruwaito.

Prof. Chukwuma Soludo, dan takarar APGA a zaben, ya samu kuri'u 4,826, Sanata Andy Uba na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu kuri'u 2,692 yayin da Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri'u 1,863.

Read also

Soludo na APGA ya bi yan takaran APC da PDP har garuruwansu ya lallasa su

Da duminsa: Soludo ya lashe karamar hukuma ta 8, ya na jagoranci da tazarar kuri'u 36K
Da duminsa: Soludo ya lashe karamar hukuma ta 8, ya na jagoranci da tazarar kuri'u 36K. Hoto daga Charles Soludo, Andy Uba da Valentine Ozigbo
Source: Facebook

A dukkan sakamakon zaben kananan hukumomi takwas da aka sanar, jam'iyya mai mulkin jihar ce kan gaba, Daily Trust ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin yanzu, kananan hukumomin da aka sanar da sakamakonsu sun hada da Orumba ta kudu, Orumba ta arewa, Njikoka, Awka ta kudu, Ontsha ta kudu, Aguata, Anaocha da Anambra ta gabas.

Soludo ya na da jimillar kuri'u 60,988 a kananan hukumomin nan takwas, Ozigbo ke biye da shi da kuri'u 24,972. Soludo ya bayar da tazarar kuri'u 36,016.

Andy Uba na jam'iyya mai mulki ne ke biye da su da kuri'u 21,505.

IGP ya bukaci sunayen 'yan sandan da har yanzu ba a biya ba a Anambra

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya umarci dukkan kwamandoji da su tattaro sunayen 'yan sandan da ke aikin zabe a Anambra kuma ba a biya su ba har yanzu.

Read also

Da duminsa: IGP ya bukaci sunayen 'yan sandan da har yanzu ba a biya ba a Anambra

Wannan ya biyo bayan korafin da wasu 'yan sanda suka yi kan cewa ba a biya su kudin alawus na zaben gwamnan Anambra ba, Daily Trust ta wallafa.

Daily Trust ta ruwaito yadda wani dan sanda da ke aiki da rumfar zabe ta takwas a gunduma ta biyu da ke Abagana, karamar hukumar Njikoka ta jihar Anambra, ya koka da rashin abinci yayin zaben.

Source: Legit.ng

Online view pixel