‘Dan takarar Gwamna, Matasan Arewa suna so Minista ya gaji kujerar Buhari a 2023

‘Dan takarar Gwamna, Matasan Arewa suna so Minista ya gaji kujerar Buhari a 2023

  • Tonye Princewill yana goyon bayan masu kira ga Rotimi Amaechi ya nemi takarar shugaban kasa.
  • An ji wata kungiyar matasa a Arewacin Najeriya tana so Ministan sufurin kasar ya karbi mulki a 2023.
  • Princewill yace ganin mukaman da Amaechi ya rike a Majalisa da Gwamnati, ya dace da shugabanci.

Rivers - Tsohon ‘dan takarar gwamna a jihar Ribas, Mista Tonye Princewill yace Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya dace da kujerar shugaban kasar Najeriya.

A ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, 2021, Punch ta rahoto Princewill yana cewa Rotimi Amaechi yana da duk abin da ake nema na zama shugaban kasa.

Tonye Princewill yana so ayi la’akari da irin abubuwan da Amaechi ya yi a majalisar dokoki, gwamnan Ribas da shugaban gwamnoni da Ministan tarayya.

Kara karanta wannan

Wasu matasan Arewa na goyon-bayan Gwamnan PDP, sun ce shi zai gyara Najeriya a 2023

Baya ga zama shugaban majalisar jihar Ribas na shekara takwas, Amaechi ya yi gwamna sau biyu har ya rike kungiyar gwamnoni, kuma tun 2015 yake Minista.

Jaridar ta rahoto Princewill a Fatakwal yana cewa Amaechi yana cikin manyan ‘yan siyasan kasar nan.

Buhari a 2023
APC tana kamfe a Sokoto Hoto: theeagleonline.com.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ra'ayin Princewill ya zo daidai da na matasan Arewa

Tsohon ‘dan takarar gwamnan ya yi wannan bayani da yake tofa albarkacin bakinsa a kan wani jawabi da ya fito daga wata kungiya ta matasan Arewacin Najeriya.

Kamar yadda jaridar Independent ta kawo rahoto, wannan kungiya ta fito tana yin kira ga Ministan sufuri na kasar ya nemi kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

“A kan kiran da matasan Arewa suke yi ga Ministan sufuri ya fito takarar 2023, ina goyon bayan wannan matasa da suka yi abin da za su iya da kansu.”

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

“An ce ba a ganin darajar waliyyi a gidansa. Amma a nan ba haka abin yake ba. Ana girmama Amaechi a gida da waje, zai iya rike Najeriya” - Princewill.

Princewill yake cewa yana kallon wadannan matasa, kuma dama akwai bukatar a ajiye son-kai, a samu wani wanda zai iya gyara kasar nan ya karbi ragamar mulki.

Yaushe APC za tayi zaben shugabanni?

A baya kun ji yadda rikicin cikin gida yake neman kawo matsala wajen shirin zaben shugabannin jam'iyyar APC na kasa saboda rigingimu a wasu jihohi.

Har yanzu babu ranar da kwamitin Mai Mala Buni zai gudanar da babban zaben shugabanni. Tun a 2020 aka sa kwamitin rikon kwarya domin ya fito da shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel