Labari da ɗumi-ɗumi: Ortom ya kaiwa Orji Kalu ziyara a gidansa da ke Abuja

Labari da ɗumi-ɗumi: Ortom ya kaiwa Orji Kalu ziyara a gidansa da ke Abuja

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya kai wa tsohon gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu ziyara a birnin tarayya Abuja
  • Wannan dai shine karo na farko da Ortom ya kai wa bulaliyar majalisar dattijan ziyara a gidansa tun bayan zamansa gwamna
  • Kalu da mai dakinsa sun yi wa Ortom tarba ta arziki sannan suka shiga wata ganawar sirri wadda kawo yanzu ba a san abind suka tattauna ba

Abuja - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Lahadi da yamma ya ziyarci bulaliyar majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu a gidansa da ke Queen Elizabeth road, FCT Abuja.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa a yayin da ya isa, Kalu da matarsa ne suka tarbi gwamnan na Benue.

Kara karanta wannan

Taron Gangamin PDP: Fastoci sun bayyana, Bala da takarar shugaban kasa, Shehu Sani kuma gwamna

Labari da ɗumi-ɗumi: Ortom ya kaiwa Orji Kalu ziyara a gidansa da ke Abuja
Ortom ya kaiwa Orji Kalu ziyara a gidansa da ke Abuja. Hoto: The Sun
Asali: Facebook

Wannan shine karo na farko da Ortom, wanda gwamna ne a jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ke ziyartar Kalu tun bayan zamansa gwamna.

Ortom da Kalu sun saka labule yayin tattaunawarsu kamar yadda ya zo a ruwayar na The Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a sanar da abin da suka tattauna ba yayin ganawarsu har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel