Gwamna Ganduje ya motsa siyasar Kano, ya taya Kwankwaso murnar kara shekara a Duniya

Gwamna Ganduje ya motsa siyasar Kano, ya taya Kwankwaso murnar kara shekara a Duniya

  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya taya Rabiu Kwankwaso murnar cika shekara 65
  • Gwamnan na jihar Kano ya yabi Kwankwaso duk da cewa an dade da jan daga
  • Masu fashin baki da nazarin siyasa a Kano sun fara maida martani a kan batun

Kano – Mai girma Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekara 65 da haihuwa.

Abdullahi Umar Ganduje ya aika wa tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso sakon taya murna a jaridar Daily Trust ta ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, 2021.

A jiye ne Sanata Rabiu Kwankwaso wanda aka haifa a shekarar 1956 ya cika shekaru 65 a Duniya.

A sakon da ya aika wa tsohon Sanatan na jihar Kano, Ganduje ya yaba da irin cigaban da madugun siyasar Kwankwasiyya ya kawo, duk da an raba gari.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

“Godiya ta tabbata ga Allah Madaukaki da ya raya ka da koshin lafiya domin mu sake ganin zagayowar wannan rana ta haihuwarka.” – Abdullahi Ganduje.

Abdullahi Ganduje ya yabi abin da ya kira doguwar alakar da ke tsakaninsa da tsohon Ministan tsaron. Bayan aikin ofis, zumunci ya shiga tsakanin ‘yan siyasar.

Gwamna Ganduje, Kwankwaso
KWANKWASO da GANDUJE a shekarun baya Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sakon da Abdullahi Umar Ganduje ya aika ya jawo wasu ‘yan siyasar Kano sun fara surutu. Sai dai ba a shekarar nan ne Ganduje ya fara aika irin wannan sako ba.

Don dole ne - Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda

Jagororin jam’iyyar APC na Kano irinsu Alhaji Abdulmajid Dan Bilki suna ganin cewa gwamnan ya aika sakon ne domin yana neman inda zai sa kan shi a siyasa.

Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda yace gwamna Ganduje ya shiga wani yanayi na gaba kura –baya sayaki, don haka dole ta sa yake kokarin neman kamun kafa.

Kara karanta wannan

Harin Goronyo: Shugaban soji ya isa Sokoto, ya nemi sojoji da su rubanya kokarinsu

Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa wanda yana cikin ‘yan tsagin Kwankwasiyya, yace hakan ya nuna Ganduje yana fuskantar barazana ne a rikicin cikin gidan APC.

Halaccin Alhassan Ado Doguwa

A jiya ake ji cewa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya yi wa wadanda yake wakilta ruwan miliyoyin kudi da kayan sana'a. 'Dan majalisar ya kashe har Naira miliyan 70.

Tun a shekarar 1999 mutanen Tudun Wada da Doguwa suke zaben Ado Doguwa. Wannan ya sa 'dan siyasar ya yi irin wannan alheri domin ya nuna masu godiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel