Mai dakin Gwamnan jam’iyyar adawa za ta sauya-sheka zuwa APC inji 'Dan takarar APC

Mai dakin Gwamnan jam’iyyar adawa za ta sauya-sheka zuwa APC inji 'Dan takarar APC

  • Andy Uba yace mai dakin gwamnan jihar Anambra za ta shigo jam’iyyar APC
  • Sanata Uba ya bayyana haka da yake martani a kan sauya-shekar Nkem Okeke
  • ‘Dan takarar Gwamnan ya yi kira ga mutane su zabi APC a zaben Nuwamba

Anambra – ‘Dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra, Sanata Andy Uba, ya yaba da sauya-shekar da Dr. Nkem Okeke ya yi zuwa APC.

Mataimakin gwamnan Anambra, Nkem Okeke ya fice daga jam’iyyar APGA, ya koma APC. Jaridar Vanguard ce ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba.

Da yake magana a kan wannan cigaba, Andy Uba yace saura uwargidar jihar Anambra, Ebelechukwu Obiano ta rage ta shigo jam’iyyar su ta APC.

A cewar Uba wanda ke neman karbe mulki daga hannun jam’iyyar APGA, mai dakin gwamna Obiano watau Ebelechukwu Obiano za ta shigo tafiyar APC.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

“Sauya-shekar da ake ta yi daga APGA, PDP da wasu jam’iyyu zuwa APC, saboda rashin iya mulkin gwamnatin PDP ne.”
“Wannan ya sa mataimakin gwamna, Nkem Okeke ya shigo APC, kuma mai dakin Obiano ta kusa shigo wa APC.” – Andy Uba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Dan takarar APC
Sanata Andy Uba Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

APGA ta gaza, a zabi APC a ranar 6 ga Nuwamba - Andy Uba

Da yake jawabin kamfe, Andy Uba ya yi kira ga musamman matasa, su fito su zabi APC a zaben gwamnan da za ayi, yace zai yi masu ayyuka idan ya yi nasara.

“Ina kira gare ku mutanen Anambra, ku zabi jam’iyyar APC a zaben 6 ga watan Nuwaban da za ayi domin a rika yi da matasan mu.”
“Za mu gyara tituna, mu samar da ayyukan yi ga matasa domin su daina zaman-kawai, kuma za a bunkasa kiwon lafiya idan APC ta ci.”

Kara karanta wannan

2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna

“Ba na yin alkawari, in saba, duk abin da na ce to ya zama dole in cika. Ba na cikin wadanda suke saba alkawuran da suka yi.” – Uba.

Uba ya yi watsi da ikirarin da ‘yan adawarsa suke yi na cewa APC jam’iyyar mutanen Arewa ce.

PDP ta tara N60m daga kudin fam

A jiya ku ka ji cewa yayin da zaben shugabannin PDP na kasa ya karaso, Jam’iyyar adawar ta samu sama da N60m daga kudin saida wa 'yan takara fam.

Jiga-jigan ‘yan siyasa za su gwabza wajen neman kujeru da mukamai a PDP a watan Oktoban nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel