2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna

2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna

  • Mataimakin gwamnan Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Gusau ya sha alwashin yin kaca-kaca da APC a jihar Zamfara a zaben 2023
  • A cewar Mahdi jam'iyyar adawa ta PDP ta kammala shiri tsaf domin kwato mulki daga hannun jam'iyyar APC mai mulki
  • Ya ce duk wani bita da kullin da gwamnatin jihar ke yi masa don kawai ya ki komawa APC tare da Gwamna Bello Matawalle ne

Zamfara - Mataimakin gwamnan Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Gusau ya bigi kirjin cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) ta shirya yin kaca-kaca da All Progressives Congress (APC ) a zaben 2023 a jihar.

Mahdi ya kuma bayyana cewa shine sabon shugaban PDP a jihar, inda yace ya hau wannan matsayi ne tun bayan sauya shekar ubangidansa, Gwamna Bello Mohammed Matawalle da magoya bayansa zuwa APC mai mulki, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Insha Allahu bana yan Najeriya zasu yi aikin Hajji, Hukumar jin dadin Alhazai NAHCON

2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna
2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna Hoto: Deputy Governor of Zamfara State
Asali: UGC

A cewarsa, yana nan yana ta shirya ma fafutukar da ke tunkarowa, inda yace duba sakatariyar jam’iyyar da yayi ya nuna shirinsa na fafatawa da jam’iyyar mai mulki a jihar.

Ya kara da cewa an kammala tsara komai a sabuwar sakatariyar PDP duk a kokarinsa na tabbatar da ganin cewa sun yi kaca-kaca da APC a zabe mai zuwa.

Ya ce:

“Bayan sauya shekar Gwamna Matawalle, mun sama wa jam’iyyar sakatariya mai kyau domin APC ta kwace dukkanin sakatariyar PDP sannan ta mayar da su ofishoshinta a jihar."

Mataimakin gwamnan ya yi korafin cewa majalisar dokokin jihar da bangaren zartarwa na jihar suna farautarsa saboda ya ki komawa APC tare da Gwamna Matawalle.

Ya yi bayanin cewa a zamanin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Magartakada Wamakko irin haka ya faru amma gwamnan waccan lokacin ya yi watsi da banbancin jam’iyya sannan suka bunkasa jihar tare da mataimakinsa har zuwa karshen mulkinsu.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da shugaban APC ya gana da shahararren gwamnan PDP

Ya kara da cewa:

“Saboda haka, menene laifi a ciki idan Gwamna Matawalle ya bani damar bin jam’iyyar da nake muradi a maimakon tursasamun bin shi zuwa APC wanda take ba akidar siyasata ba.
“Duk da kasancewana mataimakin gwamnan jihar, gwamnan ya mayar dani ba komai ba amma kuma ba wannan bane mulkin damokradiyya."

Da farko dai Legit.ng ta kawo cewa hukumar da ke kula da gine-gine a Zamfara ta aika takardar dakatar da aiki zuwa sakatariyar PDP.

Sai dai, mataimakin gwamnan ya bayyana cewa duk makirci ne don wahalar da PDP a jihar, inda yace an sa kafar wando daya tsakanin APC da PDP a jihar.

Watanni 4 da sauya-shekar gwamna zuwa APC, PDP tace ana neman rusa mata hedikwata

A baya mun kawo cewa, a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, 2021, PDP ta reshen jihar Zamfara ta fito tana cewa akwai shiri a kasa na rusa mata hedikwata a Gusau.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: APGA ta yi martani, ta bayyana dalilin da yasa mataimakin gwamnan Anambra ya sauya sheka zuwa APC

Jam’iyyar PDP mai adawa ta zargi hukumar da ke kula da gine-gine a Zamfara watau the Zamfara State Urban and Regional Planning Board da wannan aikin.

Daily Trust tace sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, Alhaji Farouk Ahmad Shattima ya shaida mata wannan da ya zanta da ‘yan jarida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel