A cikin ‘yan kwanaki, jam'iyyar PDP ta tara miliyoyin kudi daga saidawa ‘yan takara fam

A cikin ‘yan kwanaki, jam'iyyar PDP ta tara miliyoyin kudi daga saidawa ‘yan takara fam

  • A karshen watan Oktoba ne PDP za ta gudanar da zaben shugabanni na kasa
  • Kawo yanzu jam’iyyar hamayyar ta samu N63m daga saidawa ‘yan takara fam
  • Za a nemi kujerar shugabannin jam’iyya, sakatarori da ma’aji a wannan zabe

Abuja - Yayin da ake shirin gudanar da zaben shugabanni na PDP, jam’iyyar hamayyar ta samu Naira miliyan 63 daga kudin sayen fam din shiga takara.

Jaridar Vanguard tace jam’iyyar hamayyar ta tara wannan kudi ne bayan an bude saida fam din.

PDP na saida fam ga masu neman mukaman shugabannin na kasa da za ayi. Ana sa ran gudanar da gangamin zaben ne a ranar 31 ga watan Oktoba, 2021.

Akwai ‘yan takara 33 da za su gwabza wajen neman mukaman shugabancin jam’iyyar adawar.

Read also

2023: Osinbajo da Tinubu za su yi zaman farko a game da shirye-shiryen zaben shugaban kasa

Duk wanda zai shiga takarar shugaban jam’iyya zai saye fam kan Naira miliyan 5. Ana saida fam din mataimakin shugaban jam’iyya a kan Naira miliyan 3.

Rahoton yace ‘yan takarar mukamin sakatare za su biya Naira miliyan 3 a matsayin kudin fam.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar PDP
Gangamin jam'iyyar PDP Hoto: www.pulse.ng
Source: UGC

Ana saida fam na neman takarar manyan mukamai na kasa a Naira miliyan biyu. Masu sha’awar rike mukaman mataimakan shugaba za su biya N750, 000.

Daga cikin wadanda za su shiga wannan zabe da za ayi a watan nan, akwai Iyorchia Ayu (Benuwai), Ahmed Mohammed (Gombe), Umaru Bature (Sokoto).

Ragowar su ne Daniel Woyengikuro (Bayelsa) da Kamaldeen Ajibade (Kwara). Bisa dukkan alamu babu mamaki nan gaba a ji cewa wasu sun saye fam din.

Za a nemi kujeru da-dama

Wadannan mutane za su yi takarar shugaban jam’iyya, mataimakin shugaba, sakataren jam’iyya, ma’aji, sakataren kudi da mai bada shawara kan shari’a.

Read also

‘Yan wasan Kannywood sun kirkiri fim a kan rikicin Boko Haram a Arewacin Najeriya

A Arewa Hajia Maryam Ina Ciroma za ta kara da Umar Damagum. Hajia Ciroma yayin da Eddy Olafeso da Debo Olagunagba za su gwabza a yankin Kudu.

Za mu doke APGA, PDP a zabe - Sanata Ifeanyi Uba

Dazu ku ka ji cewa ‘Dan takarar Gwamnan APC, Sanata Ifeanyi Uba a jihar Anambra yana sa rai za su lashe zaben sabon gwamna da za ayi a watan Nuwamba.

Ifeanyi Uba ya zargi gwamnonin kudu maso gabas da boye nasarorin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Source: Legit.ng

Online view pixel