Gwamnonin Kudu na boye cigaban da Buhari ya kawo yankin Ibo inji Sanatan Anambra

Gwamnonin Kudu na boye cigaban da Buhari ya kawo yankin Ibo inji Sanatan Anambra

  • Andy Uba yace ana boye nasarorin da Gwamnatin APC ta kawo a jihohin yankin Kudu
  • ‘Dan takarar Gwamnan na Anambra ya zargi Gwamnoni da rufe cigaban da ake samu
  • Uba na ganin lokaci ya yi da mutanen Anambra za su hada-kai da Gwamnatin tarayya

Lagos - ‘Dan takarar jam’iyyar APC a zaben Anambra, Andy Uba, ya zargi gwamnonin Kudu maso gabas da laifin boye nasarorin gwamnatin tarayya.

Daily Trust ta rahoto Sanata Andy Uba yana cewa jihar Anambra na kewan gwamnatin tarayya bayan shekaru 16 ba ta taba dandana mulki a sama ba.

Da yake magana da manema labarai a garin Legas a ranar Litinin, 18 ga watan Oktoba, 2021, Uba yace yana sa rai jam’iyyar APC ta lashe zaben da a za ayi.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Ministoci, Hadimai da manyan ‘Yan Majalisa suna cikin matsala a wasu Jihohi

Ganin yadda manyan ‘yan siyasa suke sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, Sanata Andy Uba ya fara hango kansa a kujerar gwamnan jihar Anambra.

Uba yana ganin gwamnatin APC ta tabuka abin kirkin da ya dace ta karbe mulkin Anambra. Sanatan yace gwamnatin tarayya ta yi aikin a-yaba a ko ina.

A cewar Sanata Uba, ba a sanar da Duniya duk irin nasarori da cigaban da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo a shekaru shida da tayi a mulki.

Zaben Anambra
Buhari da 'Dan takarar APC a Anambra Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Mai yi ba fada yake yi ba - Uba

“Za a hada abubuwan da jam’iyyar APC ta yi da na sauran gwamnatoci? Iri na ne da ba mu fadin abubuwan da mu ka yi, sai su yi tsit.”
“Na yi abubuwa da yawa, amma ba na fada. Je ka ka duba, ka kwatanta.” – Andy Uba.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Sai Majalisa ta kawo dokar hana yaran mala’u yin Digiri a Jami’o’in waje - ASUU

“Za ku hada abubuwan da sauran jam’iyyun nan; APGA, PDP, YPP da abin da APC tayi a Najeriya?
“Dukkanmu ‘yan Najeriya ne. Duba abubuwan da suke faru wa a Legas.” – Uba.

Uba yana ganin mutanen Kudu ba su da damar da za su yi kukan ba a tafiya da su a lokacin da gwamnatin tarayya ta ke gina masu babbar gadar Neja ta biyu.

“Gwamnatin APC tana aiki, amma gwamnoni suna boye duk abubuwan da aka yi. Ba za su iya rufa-rufa yanzu ba, saboda da na je zan bude komai.” - Uba.

Bincike a kan Ogbonnaya Onu

Wani bincike ya nuna cewa Ministan kimiyya da fasaha na kasa, Ogbonnaya Onu ya na korar masu rike da mukamai saboda sun ki yin abin da yake so a gwamnati.

Dr. Ogbonnaya Onu yana nada wadanda ba su cancanta ba, kuma yana saba dokokin gwamnati. Ana zargin Onu da amfani da kujerarsa wajen yin abin da ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: APGA ta yi martani, ta bayyana dalilin da yasa mataimakin gwamnan Anambra ya sauya sheka zuwa APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel