An samu kwamacala a zaben APC, mutum 4 suna ikirarin sun zama Shugabannin Jam’iyya

An samu kwamacala a zaben APC, mutum 4 suna ikirarin sun zama Shugabannin Jam’iyya

  • Zaben shugabannin jiha da APC ta shirya ya bar Akwa Ibom da shugabanni rututu
  • Augustine Ekanem, Steve Ntukekpo, Douglass Pepple suna da’awar shugabancin APC
  • Amma Ita Udose yace Mr. Augustine Ekanem ne sahihin shugaban jam’iyya na jihar

Akwa Ibom - An samu hargitsi a jam’iyyar APC na reshen jihar Akwa Ibom bayan zaben shugabannin jiha da aka gudanar da ranar Asabar da ta gabata.

Jaridar Daily Trust tace mutane hudu aka samu da kowanensu ya fito yana ikirarin ya zama shugaban jam’iyyar APC a jihar Akwa Ibom bayan an yi zaben.

Rahoton ya bayyana cewa Augustine Ekanem, Steve Ntukekpo, Douglass Pepple da wani mutum daban ne suke da’awar cewa APC tana hannunsu a jihar Kwara.

Na karshen su yana tare ne da bangaren Bishop Akpan, wani fitaccen jigon APC a jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Ministoci, Hadimai da manyan ‘Yan Majalisa suna cikin matsala a wasu Jihohi

Godswill Akpabio v Ita Enang

Steve Ntukekpo ya zama 'shugaban jam’iyya' ne bayan ya samu wasu na kusa da Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio da suka zabe shi a zaben da suka shirya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Godswill Akpabio ya yi gwamna na shekaru takwas a PDP kafin ya koma jam’iyyar APC.

Shugabannin Jam’iyyar APC
Manyan APC wajen kamfe Hoto: bcos.tv
Asali: UGC

Sannan kuma bangaren Sanata Ita Enang sun gudanar da na su zaben shugabannin, suka tsaida Douglass Pepple a matsayin shugaban APC mai hamayya a jihar.

Sanata Ita Enang shi ne mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin majalisa. Kafin nan hadimi ne a kan harkokin majalisar dattawa.

Akwa Ibom: Dr. Ita Udose ya raba gardama

Da yake bayani a jiya, shugaban APC na rikon kwarya, Dr. Ita Udose ya bayyana Augustine Ekanem a matsayin sahihin shugaban jam’iyyar APC da ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Jerin wadanda suka yi nasara a zaben shugabancin jam'iyyun APC da PDP na jihohi

“Kamar yadda tsarin mulkin APC ya yi tanadi, ina so in sanar da jama’a da ‘ya ‘yan jam’iyya sakamakon zaben da aka shirya a Sheergrace Arena, Uyo, Akwa Ibom.”

Ita Udose yace kowane bangaren jam’iyya sun halarci wannan zabe da ya ba Augustine Ekanem nasara. APC na fama da irin wannan rigima a wasu jihohin da-dama.

PDP ta garzaya kotu a jihar Zamfara

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta dauko babban lauya O.J. Onoja ya tsaya mata a kotun tarayya yayin da ta kai kara, tana so a karbe kujerun duk wani wanda ya koma APC.

Kamar yadda ku ka ji labarin idan PDP ta dace a kotun da ke zama a Abuja, APC ta na iya rasa kujeru sama da 30. Daga ciki har da na gwamnan jihar da Sanatoci uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel