Rikicin APC: Shekarau ya bayyana makasudin kai korafin Ganduje gaban Shugabannin APC na kasa

Rikicin APC: Shekarau ya bayyana makasudin kai korafin Ganduje gaban Shugabannin APC na kasa

  • Ibrahim Shekarau ya yi magana bayan sun zauna da shugabannin APC a Abuja
  • Sanatan Kano ta tsakiya ya yi jawabi a madadin masu fada da gwamnatin Kano
  • Wasu ‘Yan APC su na karar Gwamnatin Kano, sun ce an maida su saniyar ware

Abuja - A halin yanzu sabani ya shiga tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen jihar Kano, inda aka ja daga tsakanin gwamnati da wasu ‘yan majalisu.

Wannan rikicin ne ya jawo ‘yan majalisar tarayya da wasu manyan ‘yan siyasa daga jihar Kano suka gana da shugabannin jam’iyyar APC na kasa dazu.

Yahuza Ahmad Getso ya wallafa takardar korafin da ‘yan tawaren suka gabatar wa shugabannin rikon kwaryan APC karkashin jagorancin Mai Mala Buni.

Wadannan ‘yan taware da wasu suka kira su ‘Rescue Kano Coalition’ sun bukaci kwamitin CEPC ya yi maza ya shawo kan sabanin da ake samu a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Ministoci, Hadimai da manyan ‘Yan Majalisa suna cikin matsala a wasu Jihohi

Menene kukan Rescue Kano Coalition?

A korafin, wadannan ‘yan siyasa sun ce an yi rashin adalci wajen gudanar da zaben jam’iyyar APC na mazabu da kuma kananan hukumomi a kwanakin baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Takardar korafin tace wannan ya jawo wasu ‘yan taware suka je gefe, suka zabi shugabanninsu.

Shekarau da mutanensa
'Yan tawaren RKC Hoto: Ahmad Gandujiyya
Asali: Facebook

‘Yan tafiyar Rescue Kano Coalition sun ce ba za su yarda a shirya irin zabukan da aka yi a baya a babban zaben shugabanni na jiha da za a gudanar nan gaba ba.

Haka zalika ‘yan tawaren sun yi kira ga shugabannin APC su duba lamarin, kuma su dauki mataki.

A cewar wadannan kusoshi na APC, gwamnatin Kano ba ta shawara da Sanatocin jam’iyya, haka zalika ta yi watsi da sauran masu ruwa da tsaki a tafiyar APC.

A wani bidiyo da Muaz Magaji ya wallafa, an ji Sanata Ibrahim Shekarau ya na magana da ‘yan jarida a madadin ‘yan majalisar da sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya tana biyan malaman jami’a N6, 000 rak a matsayin albashin karshen wata

Ibrahim Shekarau yace sun kawo kukansu ne gaban uwar jam’iyya, kuma suna sa rai za ayi wani abu.

Siyasar Anamabra ta fara rikida

An ji cewa Mataimakin gwamnan jihar Anambra, Dr. Nkem Okeke, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin kasa a ranar laraba, 13 ga watan Oktoba, 2021.

Nkem Okeke ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja. Shugaban APC, Mai Mala Buni da Hope Uzodinma ne suka yi masa rakiya.

.

Asali: Legit.ng

Online view pixel