“MIliyan 3 Zan Sayar” : Wani Mutum Daya Fito da Mota “1974 Volkswagen Beetle”

“MIliyan 3 Zan Sayar” : Wani Mutum Daya Fito da Mota “1974 Volkswagen Beetle”

  • Dan Najeriya ya janyo kace-nace a dandalin sadarwa na Twitter bayan ya fito da tsohuwar mota samfurin “1974 Volkswagen Beetle car”
  • Ya daura hoton motar ne a shafin san a Twitter ne tare da cewar yana fatan ganin ya saida ita miliyan 3 ne ga mai bukata
  • Mutane da yawa masu amfanki da dandalin na Twitter sun cika da mamaki da cewa ba suyi zaton har yanzu za’a samu irin wannan motar ba

Wani mutum dan Najeriya daya wallafa zafafan hotunan wata tsohuwar mota da akayi yayi a 1974 mai suna Volkswagen Beetle ya tayar da kura wanda har yasa hotunan motar ya karade yanar gizo-gizo ya kuma kawo kace-nace.

Mutumin mai suna Uchenna Odu, ya kara da cewar, motar tasa ta siyarwa ce saboda haka ne ma yake gayyatar mutane da su zo su siya idan tayi musu.

Uchenna Odu yace burin sa shine ya sayar da motar akan kudi wuri na gugun wuri har naira miliyan 3, inda yace duk mai son dandana salon mazan jiya, ya iya zuwa ya siya domin tuna baya.

1974 Volkswagen Beetle
Motar ta tafi da zuciyar mutane Hoto: Twitter/@maziechidiime. Asali: Twitter
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hotunan 1974 Volkswagen Beetle sun karade ko ina shafin yana gizo-gizo kuma sun kawo cece-kuce

Ita dai motar samfurin “1974 Volkswagen Beetle” da ake mata kirari da “Kande ba Duwaiwai” da Hausa, anyi mata shudin fenti ne watau blue. Kuma Uchenna yace sai da yayi mata rijista kamar motar wannan zamanin.

Bai dade da yin wannan rubutun akan motar bane, mutane suka soma tofa albarkacin bakin su. Inda wasu suka ce, ai atafau basu taba zaton a yau za'a samu irin motar nan ba.

Hakan tasa, wasu nan da nan suka koma tuna lokacin yarintar su, watau lokacin da ake yayin motar ta alfarma a wancan lokaci.

Tun yaushe motar ta karade dandalin sadarwa na zamani, yayin da a wani bangare kuma wasu mutane suka dinga zubo zantuka masu ban sha’awa da ban dariya.

Ga cikakken abinda Uchenna ya Wallafa a dandalin:

Volkswagen
“MIliyan 3 Zan Sayar” : Wani Mutum Daya Fito da Kwararrababbiyar Mota da Samfurin “1974 Volkswagen Beetle”
Asali: Twitter

Fassara:

“Ugochukwu
Mu koma zamanin daya shude. A zo a siya wannan hadaddiyar motar samfurin 10974 na Volkswagen Beetle mai rijista, Farashi N3,000,000” injishi

Masu bibiyar wallafar sun bayyana raayin su daga Twitter, Ga Kadan daga ciki:

@nairawall cewa yayi: " Wahala bata ishe kaba kenan, bani da karfin da zan iya sarrafa sikiyarin motar”
@Odi_richi yace: "Sai kuma naga motar da lambar motar jos…jihar da aka haife ni aka raine ni.”
@obanyanwu yace: "Azubuike akan 3m? Mazi kada kasa jinni na yahau."
@DavidKing77777 cewa yayi: "Wato wannan motar samfurin Volkswagen beetle da kuke gani, a shekaru kadan masu zuwa, Miliyan 10 million ta bazata iya siyan ta ba. Kayan tarihi ne wannan, wasu kamfanin nikan fim zasu iya neman kayan tarihi domin yin amfani dashi a fim nasu. Idan na samu kudi, zanyi amfani da ita wajen zuwa ganin surukaina……SHEKPA.”

@arthurtelfair8 cewa yayi: " Motar nan tabbas tafi 3m a wasu kasashen. A kasar waje zasu iya holing ta akan $50k zuwa sama.

@Easyfunk ya fada cikin mamaki: " Tab, ai motar nan tayi mugun arha, domin ta tarihi ce. Fatan nasara wajen siyarwa!’ inji shi.

Wata Matashiyar ta Tsinci Talabijin Din KaKanta

A wani labari makamancin wannan, wata matashiya ta tsinci tsohuwar ajiyar kankanta da ta dade a boye.

Jaridar Legit ta ruwaito cewar, TV din ta kakanta ce, kuma ta jima sosai a ajiye ba tare da anyi amfani da ita ba.

A hoto mai motsi data wallafa , matashiyar tace an sayi talabijin din ne a shekarar 1970, wato kimanin shekaru hamshin da uku kenan.

Tuni itama mutane suka dinga tofa albarkacin bakin su tare da nuna sha'awar su ta siyan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel