Bidiyon Yadda Wata Mata Ke Tallan Maganin Gargajiya a Kan Babur Ya Ba Jama’a Mamaki

Bidiyon Yadda Wata Mata Ke Tallan Maganin Gargajiya a Kan Babur Ya Ba Jama’a Mamaki

  • Bidiyon wata mata da ke siyar da maganin gargajiya irin na Yarbawa ya yadu a kafar sada zumunta
  • A bidiyon, an ga lokacin da matar ke kan babur tana tukawa dauke da daron tallan maganinta a ka
  • Jama’a sun shiga mamakin yadda ta iya daukar daron a ka yayin da yake tukin babur a kan titi

Wata mata da ke tallan fitaccen maganin gargajiya irin na Yarbawa ta jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta TikTok.

Wannan ya faru ne bayan da aka yada bidiyon matar a lokacin da take yawo a kan babur tana tallata hajarta.

A bidiyon da @keyrankader_ ya yada, an ga matar ta makare daronta da magani, sannan ta hau babur ba tare da rike daron da ke kanta ba.

Bidiyon mata mai tallan magani a kan babur
Yadda mai tallan magani ke yi a kan babur | Hoto: @keyrankader_.
Asali: TikTok

Yadda ta yadu a TikTok

Babban abin da ya fi jan hankalin jama’a shine yadda ta jera gorunan maganin kana ta daura daron a kanta ba tare da wata matsala ba tana tuka babur.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama’ar TikTok sun shiga mamaki, inda suka bayyana al’ajabin yadda matar mai shekaru ke sana’arta.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a TikTok

@Solant ya ce:

"Jarumar uwa kenan.”

@asanesako571 yace:

"Bayan wasan jiya, na ga wannan matar a kan hanya.”

@David Ibrahim yace:

"Tsohuwar uwa, ina mika jinjina ta.”

@solfridkas yace:

"Wannan shi ne zahirin abin da ake nufi da mace mai karfi.”

@losseni yace:

"Na ma rasa me zance.”

@godbless yace:

"Tana karfi kam.”

@guykowasky yace:

"Idan na auri wannan matar, ko da ace za ta tambayi miliyan 300, zan iya ba ta kati na cikin sauki.”

@valeriesimy yace:

“Gaskiya muna bukatar taimakawa wannan matar.”

Bidiyon yadda matashi ya kai budurwarsa shagon gwanjo

A wani labarin, kun ji yadda wani matashi ya dauki budurwarsa ya kai ta rumfar siyar da kayan gwanjo domin ta zabi wanda ya yi mata ya biya kudin.

An san mata da kwalisar siyan kayayyaki masu tsada, musamman a irin wannan zamanin, amma wannan budurwar bata nuna damuwa da wannan lamari mai daukar hankali ba.

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi mamaki, sun bayyana martaninsu game da wannan yanayi da matashin ya nuna na kai abar kaunarsa domin sayen kayan da aka riga aka saka su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel