"Ba Hannun Kwankwaso", Baban Chinedu Ya Bayyana Wadanda Ya Ke Zargi Da Kai Masa 'Hari' Bayan Zaben Gwamna Kano

"Ba Hannun Kwankwaso", Baban Chinedu Ya Bayyana Wadanda Ya Ke Zargi Da Kai Masa 'Hari' Bayan Zaben Gwamna Kano

  • Fitaccen jarumin Kannywood, mawaki kuma mai wasan barkwanci, Yusuf Haruna da aka fi sani da Baban Chinedu ya magantu kan barnar da aka masa bayan zaben gwamnan Kano
  • Baban Chinedu ya ce baya zargin Sanata Rabiu Kwankwaso ko Abba Gida-Gida, zababben gwamnan Kano, sai dai wasu yan Kannywood da ke masa hassada
  • Mai wasan barkwancin ya ce an fada masa wasu da suka rufe fuska ne suka jagoranci kai harin da aka masa asarar a kalla N10m, ya kara da cewa jami'an tsaro na bincike

Yusuf Haruna, shahararren jarumin Kannywood, mawaki kuma mai wasan barkwanci, a masa'antar fina-finai da aka fi sani da Baban Chinedu ya magantu kan harin da aka kai masa a baya-bayan nan.

Baban Chinedu ya kore zargin da aka yi na cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya aika yan daba su tafi su lalata masa kaya da na abokin aikinsa Rarara cikin wata hira aka yi da shi.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Min Tayin N100m Don In Janye Takara, Dan Shekaru 33 Da Ya Kayar Da Kakakin Majalisar Yobe

Babban Chinedu
Baban Chinedu ya ce lalata masa kaya da aka yi bayan zabe ba ta da alaka da siyasa ko Kwankwaso. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai wasan barkwancin ya furta hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi game da harin da aka kai wa kayayyakinsa a Kano yayin rikicin bayan zabe a ranar 18 ga watan Maris, rahoton Daily Trust.

Da ga cikin kalamansa, ya ce:

"Mutane suna kira suna min jaje suna cewa Kwankwaso ya aika yan daba su lalata kaya na da na Rarara amma ina fada musu Kwankwaso da zababben gwamnan Kano ba su da hannu.
"Wannan aikin wasu mutane ne da suka san mu sosai kuma ba su farin ciki da nasarorin da muka samu kawo yanzu."

Na yi asarar kaya na kimanin Naira miliyan 10

Da aka tambaye shi adadin abin da ya rasa, Baban Chinedu ya ce an lalata masa firinji, kayan kida na sutudiyo da wasu kayayyaki masu daraja da kudinsu ya haura naira miliyan 10.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Ina zargin yan uwan mu na Kannywood suka kai harin, Baban Chinedu

Ya kara cewa yana zargin wasu cikin yan Kannywood da ke masa hassada saboda nasarorin da ya samu ne suka kai masa harin amma dai jami'an yan sanda suna bincike kuma gaskiya zai fito fili daga bisani.

"An fada min cewa wasu mutane da suka rufe fuskokinsu don kada a gane su ne suka yi wa yan daban jagora. Kuma kayan mu kadai aka ware aka lallata. Na san abin da na ke cewa, akwai wani cikinsu ya ce za su aikata abin da aka min bayan zabe."

Matashi Ya Kayar Da Kakakin Majalisa Wanda Ya Yi Fiye Da Shekaru 20 Kan Kujerar Wakilci a Majalisar Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa Honarabul Ahmed Mirwa Lawan ya sha kaye a hannun matashi Lawan Musa na jam'iyyar PDP, mai wakiltar Nguru II.

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel