Matar Aure tayi wa Mijinta Ihu, Diyarsu ta Kai Mata Cizo a Bidiyon don Tarewa Mahaifinta

Matar Aure tayi wa Mijinta Ihu, Diyarsu ta Kai Mata Cizo a Bidiyon don Tarewa Mahaifinta

  • Wata uwa ta nuna irin matukar kaunar da 'diyarta ke wa mahaifinta yayin da tayi yunkurin masa ihu cike da fada
  • Don ganin yadda 'diyarta za ta yi, matar ta nuna kamar tana fada da mijinta inda ta rike masa hannu tare da masa ihu
  • Masu amfani da dandalin sada zumunta sun ga irin yadda yarinyar ta ciji mahaifiyarta a hannu, lamarin ya ba jama'a dariya

Wata uwa, #mafaldagomes004, ta wallafa wani bidiyo mai ban dariya a dandalin TikTok don nuna yadda 'diyarta ke kula da mahaifinta da kuma irin shakuwar dake tsakaninsu.

A wani gajeren bidiyo, mahaifiyar ta nuna kamar tana fada da mijinta wanda yake dauke da 'yar yarinyar. A lokacin da mahaifiyar ta kama hannun mutumin kamar tana dukansa, yarinyar ta shigar mishi fadan.

Kara karanta wannan

Da Kaina na Ja Masa: Budurwa Ta Tafkawa Tsohon Saurayinta Asiri da Jininta Kan Kin Karbar Cikin da Yayi Mata

Yarinya
Matar Aure tayi wa Mijinta Ihu, Diyarsu ta Kai Mata Cizo a Bidiyon don Tarewa Mahaifinta. Hoto daga TikTok/@mafaldagomes004
Asali: UGC

A matsayin hanyar dakatar da mahaifiyar, 'yar yarinyar ta ciji mahaifiyarta a hannu. Mutane da dama sun yi mamakin matakin da yarinyar ta dauka.

Iyaye da dama sun garzaya sashin tsokacin mahaifiyar, wadanda suka ce yarinyar tayi amfani da iya abun da yake da shi a kasa ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga lokacin da aka tattara wannan rahoton, bidiyon ya tara sama da tsokaci 2,000 da jinjina sama da 70,000.

Jama'a sun yi tsokaci

Ga wasu daga cikin tsokacin:

MaMpo ta ce:

"Abun da birgewa yadda tayi amfani da abun da take da shi a kasa, hakora maimakon mari."

A.Adekunle ta ce:

"Akwai wani abun birgewa game da 'yan yara da iyayensu maza."

Chandra Leonard ta ce:

"Abun dariya! Ta yadda ta riga ta san yadda suke fada tana 'yar karamarta."

Kara karanta wannan

Mahaifi da Yaronsa Sun Hadu Sun Jibgi Ma’aikata Saboda Uwarsu Ta Rasu a Asibiti

curb_ur_criticism ta ce:

"Tunaninta shi ne yadda za ta kare shi ta kowacce hanya."

Eroline ta ce:

"Mama ba wasa take ba, ta san ita ba 'diyarki bace, gimbiyar baba ce."

stir baby ta ce:

"Gimbiya ya fada mata babu wanda zai kara da baba ya tafi lafiya."

user5082316002323 ta ce:

"Irin yadda nake kaunar mijina, ina jin tsoron haifar mace."

Budurwa ta tafkawa tsohon saurayinta asiri, ya daidaice

A wani labari na daban, wata budurwa ta bayyana yadda ta tafkawa saurayi asiri bayan ya ki karbar cikin da ya dirka mata.

Ta sanar da cewa har yanzu bai yi aure ba balle ya haihu kuma yana bin titi yana tsince-tsince.

Asali: Legit.ng

Online view pixel