'Dinkin da na bayar daban da wanda Tela ya min, wata ‘yar Najeriya ta koka

'Dinkin da na bayar daban da wanda Tela ya min, wata ‘yar Najeriya ta koka

A cikin wannan dan tsukukun wanda shagulgula su ka yawaita, mutane su na ta kokarin dinka sutturu masu burgewa.

Sai dai teloli ba su daina yin dinkunan da su ka ga dama ba kamar yadda wannan labarin ya nuna.

'Dinkin da na bayar daban da wanda Tela ya min, wata ‘yar Najeriya ta koka
Yar Najeriya ta koka kan dinkin da ta bayar da abin da tela ya dinka mata. Hoto: Photo credit: @toh_yor_c
Asali: Instagram

Wata ‘yar Najeriya mai suna toh_yor_c ta zama abar dariya bayan ta yi wata wallafa a shafinta na Twitter.

A wallafar, ta sa hoton asalin rigar da ta nuna wa tela kuma ta biya shi duk kudaden da ya dace ta bayar na dinkin.

A hoton, rigar ta na da wani hannu mai kayatawar wanda wata kyakkyawar budurwa sanye da rigar mai dammarar zamani ta sa cike da burgewa.

Kara karanta wannan

'Dan Sanda Abokin Kowa: Lokuta 4 da ƴan sandan Najeriya suka yi wa mutanen da basu sani ba manyan abin alheri

Sai dai daga karshe, wacce ta yi wallafar ta nuna rashin jin dadinta akan yadda telan ya dinka tata rigar.

Nan da nan mutane su ka fara tsokaci a karkashin wallafar

funjet01:

“Buba da zani tare da wata dammara kamar za a zubar da ciki.”

nikky_owokoya ta ce:

“Har sanya wani abu can daban ya yi wanda ba ki bukata ba.”

desoyin1_ ya ce:

“Kamar rigar mutanen farko.”

bibreola_bespoke ta ce:

“Tun da wuri haka? Ya yi sammako da fara wannan cikin sabuwar shekarar nan.”

bunmiomolaraojo ta ce:

“Wasu telolin ba za su shiga aljanna ba.”

caxxue_ ta ce:

“Wannan riga haka kamar manomi ya dinka.”

flakisflakes ya ce:

“Ya kamata teloli su dinga jin tsoron Allah.”

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Ministan Buhari ya fitar imel dinsa, ya roki 'yan Najeriya su fadi ra'ayinsu akan aikinsa

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel