Dr Dre ya shirya ƙasaitacciyar liyafar rabuwa da matarsa har da ƙawata gidansa da balan-balan

Dr Dre ya shirya ƙasaitacciyar liyafar rabuwa da matarsa har da ƙawata gidansa da balan-balan

  • Furodusan wakoki, Dr. Dre ya shirya liyafa ta musamman bayan an katse igiyar aurensu mai shekaru 21 da tsohuwar matarsa, Nicole Young
  • Ya dauki hoto a gaban wasu balan-balan da aka jera su tare da rubuta “Divorced AF” wato “mun rabu” bayan rabuwarsa da tsohuwar matarsa
  • Tun watan Yunin 2020, matar ta bukaci su rabu sannan ta bukaci ya biyata dala biliyan daya, liyafar da ya shirya na nuna sun samu matsaya

Mawaki kuma furodusan wakoki, Dr. Dre ya yi shagalin komawa gwauro bayan kwashe shekaru 21 da auren Nicole Young.

Yanzu aurensu ya rabu amma har yanzu ana ta tirka-tirka akan batun yarjejeniyar raba kudade tsakaninsu, TMZ ta ruwaito.

Dr Dre ya shirya ƙasaitacciyar liyafar rabuwa da matarsa har da ƙawata gidansa da balan-balan
Dr Dre ya shirya biki na rabuwa da matarsa bayan sun shafe shekaru suna fafatawa. Photo credit: therealbreyonprescott
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar

Yanzu haka Young ta na ta neman yadda za a halasta yarjejeniyar raba dukiya da ma’aurata su ke yi idan za su rabu, kuma idan hakan ya tabbata sai sun raba komai gida biyu.

A ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba, abokin Dre, Breyon Prescott ne ya wallafa hotonsa a Instagram gaban wasu balan-balan da aka jera wadanda aka rubuta “Divorced AF” ma’ana, “mun rabu”.

An ga Dre cike da farin ciki

An ga Dre cike da farin ciki da annashuwa a fuskarsa yayin da ya baza kafadunsa ya na nuna murnarsa.

Prescott ya yi tsokaci a karkashin wallafar inda ya ce:

“Dan ‘uwa Dre ya sanar da ni cewa sun tsayar da magana! Barka Dre.”

Dre ya dade su na rikici da matarsa tun bayan ta bukaci rabuwar aurensu a watan Yunin 2020, inda ta bukaci a biya ta dala biliyan daya.

Sai dai alamar “Divorced AF” na nuna cewa Dre da Nicole sun kai wata matsaya. Har yanzu su na ci gaba da rikici akan batun raba dukiyarsa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Tsohuwar matarsa ta ce sun yi yarjejeniyar a lokacin aurensu

Bayan Young ta bayyana yadda su ka sa hannu akan takardun raba dukiya a lokacin aurensu a shekarar 1996, ta ce Dre ya yaga takardun bayan shekaru kadan da auren.

Furodusan ya musanta maganarta da kuma batun raba dukiyar. Ko da sun yi yarjejeniyar, ba za ta mallaki rabin dukiyarsa ba sai dai tallafi na ma’aurata da zai iya bata.

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun fito da sabon salo a Zamfara, sun saka sabon haraji

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel