Tsoho dan shekara 71 ya mutu yayin Jima'i da yarinya yar gidan magajiya a Shagamu

Tsoho dan shekara 71 ya mutu yayin Jima'i da yarinya yar gidan magajiya a Shagamu

  • An tsinci gawar wani mutumi da ya mutu dakin yarinya a jihar Ogun
  • Majiyoyi sun bayyana cewa yana cikin lalata yayi numfashinsa na karshe
  • Yan sanda sun yi awon gaba da gawarsa zuwa asibitin Sagamu

Sagamu, Ogun - Wani tsohon dan shekara 71 mai suna Ajibola Olufemi Adeniyi ya mutu yayin lalata da wata 'yar gidan magajiya cikin dakin Otal a garin Shagamu dake jihar Ogun.

Punch ta ruwaito cewa wannan mumunan lamari ya faru ne a Otal mai suna /50 hotel Ogijo, karamar hukumar Sagamu.

Mamacin, wanda mazaunin gida mai lamba 22, Akilo Street, Bariga, jihar Legas ya ziyarci gidan magajiyar domin hutawa tare da wata yarinya mai suna Joy.

Wata ma'aikaciyar dakin Otal din wacce ta bukaci a sakaye sunanta tace:

Read also

Da duminsa: Bam ya hallaka akalla mutum 32 a Masallacin Shi'a a ​kasar Afghanistan

"Yayinda yake cikin jima'i, kawai ya yanke jiki ya mutu kai tsaye."

Wata majiya ta bayyanawa Punch cewa jamian yan sandan ofishin Ogijo sun ziyarci wajen don dauke gawar Adeniyi.

Majiyar tace:

"Yayinda ake kokarin neman iyalansa, an ajiye gawarsa a dakin ajiye gawawwakin asibitin Shagamu, jihar Ogun."
"Yan sanda sun garkame yarinyar domin sanin abinda ya yi sanadiyar mutuwarsa."

Tsoho dan shekara 71 ya mutu yayin Jima'i da yarinya yar gidan magajiya a Shagamu
Tsoho dan shekara 71 ya mutu yayin Jima'i da yarinya yar gidan magajiya a Shagamu
Source: UGC

Source: Legit.ng News

Online view pixel