Rayuwa ba Tabbas: El Rufai Na Tsare, an Yi Babban Rashi a Iyalansa a Ranar Sallah

Rayuwa ba Tabbas: El Rufai Na Tsare, an Yi Babban Rashi a Iyalansa a Ranar Sallah

  • An shiga jimami a cikin iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai bayan mutuwa ta dauki daya daga cikin mambobin iyalin
  • Dan majalisar da ke wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilai, Mohammed Bello El-Rufai wanda da ne ga Nasir El-Rufai, ya sanar da rashin da aka yi a ranar Juma'a
  • Bello El-Rufai ya bayyana cewa an yi babban rashi inda ya bukaci jama'a da su sanya marigayiyar a cikin addu'o'insu

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Mutuwa ta ratsa iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Allah ya yi wa matar yayansa, Safiya Ali Rufai, rasuwa a ranar Sallah bayan ta yi jinyar rashin lafiya.

Matar yayan El-Rufai ta riga mu gidan gaskiya
Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilai, Mohammed Bello El-Rufai, ya sanar da hakan a shafinsa na X a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Bayan sanarwar Saudiyya, Sarkin Musulmi ya fadi ranar da za a yi karamar Sallah a Najeriya

Wacece ta rasu a iyalan El-Rufai?

Bello El-Rufai ya bayyana cewa marigayiyar ta kasance mata a wajen yayan mahaifinsu wanda ake kira da Baba Ali Rufai, wanda shi ma ya riga mu gidan gaskiya.

Dan majalisar wanda yake da ne a wajen El-Rufai ya bayyana cewa marigayiyar ta rasu ne a ranar Sallah bayan ta yi 'yar gajeruwar jinya.

"Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un. Allah ya jikan mahaifiyarmu, Gwaggwo Safiya Ali Rufai. Abin baƙin ciki ta riga mu gidan gaskiya a yau ranar Sallah bayan rashin lafiya na ɗan lokaci."
"Wannan wata tunatarwa ne kan yadda rayuwa take mai saurin karewa. Za a yi rashinta ƙwarai da gaske. Ta kasance matar marigayi mahaifinmu ne, Air Vice Marshal, (Baba) Ali Rufai."
"Shi ne babban wa ga mahaifinmu abin ƙauna, Mallam Nasir El-Rufai, kuma shugaban iyalinmu, Baba Bashir El-Rufai."
"Gwaggwo Safiya mace ce mai jajircewa, mai tarbiyya, mai zurfin addini, kuma mai yawan tausayi. Mahaifiya ce ga mutane da dama. Ta kasance mai tsaurarawa wurin ganin an yi tarbiyya. Za a yi rashinta sosai."

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

- Mohammed Bello El-Rufai

Bello ya bukaci a yi mata addu'oi

Dan majalisar ya kuma bukaci jama'a da su yi wa marigayiyar addu'ar samun rahama a wajen Allah madaukakin sarki.

"Ina roƙon jama'a da su taya mu addu'ar Allah Ya sanya ta samu gida a gidan Aljanna. Allah ya ji kan dukkan masoyanmu da suka riga mu gidan gaskiya. Allah ya ƙara mana haƙuri."
"Allah ya jikan Yaya Zainabu da Yaya Farida. 'Ya'yanta mata guda biyu waɗanda suka rasu shekaru da suka gabata. Lallai, Allah ne mafi sani."

- Mohammed Bello El-Rufai

Mutuwa ta ratsa iyalan Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

El-Rufai ya samu nasara a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya samu nasara a wata kara da ya shigar gaban kotu.

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Kaduna ta soke hukuncin da kotun tarayya ta yanke a wata kara da tsohon gwamna, Nasir El-Rufai, ya shigar a kan majalisar dokokin jihar.

A hukuncin da kotun ta yanke kan ƙorafin daukaka karar, kotun ta bayyana cewa an samu kura-kurai a shari’ar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuli, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng