Yadda Masu Sukar Musulunci Suka Sa Baban Chinedu Ya Ajiye Fim zuwa Wa'azi

Yadda Masu Sukar Musulunci Suka Sa Baban Chinedu Ya Ajiye Fim zuwa Wa'azi

  • Yusuf Haruna da aka fi sani da Baban Chinedu ya yi karin haske game da yadda ya sauya daga dan fim zuwa mai wa'azin addinin Musulunci
  • Ya bayyana cewa ya daina rawa da waka tun bayan da ya shiga harkar wa'azi, ya kuma fadi dalilan da ya sa ake ganinsa a sababbin fina-finai
  • Baban Chinedu ya ce bai yi tsammanin al'umma za su karbe shi hannu biyu-biyu ba idan ya fara wa'azi saboda harkar fim da ya dade yana yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tsohon dan fim, Yusuf Haruna da aka fi sani da Baban Chinedu ya yi hira game da yadda ya samu kansa a harkar wa'azin Musulunci.

Ya bayyana cewa shi ma ya samu kansa a hakar ne kamar a mafarki, inda ya dawo mai wa'azin addinin Musulunci ba tare da ya tsara hakan ba.

Kara karanta wannan

'Dalilin yi wa jam'iyyar PDP Al Kunut a shekarun baya': Sheikh Isa Pantami

Baban Chinedu yayin wa'azi a jihar Gombe
Lokacin da Baban Chinedu ya zo wa'azi Gombe. Hoto: Sheikh Adam Muhammad Albani.
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro maganganun da Baban Chinedu ya yi ne a wani bidiyo da tashar DW Hausa ta wallafa a Facebook bayan hira da shi.

Dalilin shigar Baban Chinedu wa'azi

An tambayi Baban Chinedu kan dalilan da ya sanya shi sauyawa daga harkar fim da waka zuwa mai wa'azin addinin Musulunci, sai ya ce:

"Yadda ka ke mamaki nima haka nake mamaki, kawai yadda ka san an kunna wuta an kashe haka na samu kaina. Ban taba shirya cewa zan koma da'awa ba."

Ya kara da cewa:

"Na san cewa dai Allah ya ba ni ilimin da suka shafi adinai daban-daban bayan Kiristanci. Abin da ya kai ni (wa'azi) ganin wasu mutane da yadda ake yi wa Musulunci zagon kasa.
"Kuma wasu maganganu ne wanda babu dadi, za ka ga ana kokarin a dauki matasa domin a batawa Musulunci suna.
"Ina ganin ina da amsar da zan ba masu yin irin wannan, in na tuna ni dan fim ne sai na hakura. Ban yi tunanin za a saurara ba, za a ce wasan kwaikwayo ne.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gyara halin tubabbun 'yan ta'adda sama da 100, za su dawo cikin mutane

Baban Chined da tare da Dr Ahmad Gombe
Dr Ahmad Gombe tare da Baban Chinedu a wajen wa'azi. Hoto: Sheikh Adam Muhammad Albani Gombe.
Source: Facebook

Baban Chinedu ya rabu da fim

Baban Chinedu ya bayyana cewa ya riga ya bar fim duk da cewa har yanzu yana da alaka da wasu 'yan wasan kwaikwayo da suka yi aiki tare.

Ya kara da cewa kallonsa a fim din Gidan Badamasi da ake ya samo dalili ne kasancewar an dauki fim din sama da shekara a baya, amma yanzu ya rabu da waka da fim.

Duk da haka, Baban Chinedu ya ce idan akwai fim da zai karasa shi ne alkawarin da ya yi wa Gidan Badamasi, inda ya ce ya sanya hannu a baya zai karasa musu wani shiri.

Ana so Rarara ya taimaki Baban Chinedu

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Muhammad Adam Albani Gombe ya yi kira ga mawaki Dauda Kahutu Rarara ya taimaka wa Baban Chinedu.

Albani Gombe ya yi kira ga Rarara ne a wani wa'azi da Adam Ashaka da Baban Chinedu suka yi a masallacin Miyetti a jihar Gombe.

Malamin Musuluncin ya bayyana cewa ya san Rarara ya saba yin ayyukan alheri a baya, amma watakila ba a taba isar masa da irin bukatar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng