An Yi Gobarar Dare, Wuta Ta Tashi a Kasuwar Singer a Kano
- Wata mummunar gobara ta tashi a Kasuwar Singer da ke birnin Kano da misalin ƙarfe 3:00 na asuba, lamarin da ya jefa jama'a a cikin tashin hankali
- Kungiyar 'yan kasuwa ta KAMCHAFA ta tabbatar da faruwar lamarin tare da miƙa saƙon jaje ga 'yan kasuwa da suka yi asarar miliyoyin Nairori
- Duk da ba a kai ga sanin dalilin tashin gobarar ba, amma an tabbatar da cewa ta lakume shaguna da dukiyoyi masu tarin yawa zuwa yanzu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar Yan kasuwa ta Kano Markets Chairmen Forum Association (KAMCHAFA) ta tabbatar da aukuwar wata mummunar gobara a kasuwar Singer da ke kano.
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Ambasada Kabiru Musa Haruna, Mai magana da yawun Kano Markets Chairmen Forum Association (KAMCHAFA) ya fitar a ranar Litinin, 2 ga watan Fabarairu, 2026.

Source: Facebook
Sakon da ya wallafa a shafin kungiyar na Facebook, Kabiru Musa Haruna ya ce labarin ya yi masu muni matuka, tare da mika sakon jaje ga takwarorinsu da asarar ta shafa.
Yadda gobarar ta tashi a kasuwar Kano
A cewar sanarwar, an samu labarin mummunar gobarar da ta tashi da 3:00 na asubahin ranar Litinin a Kasuwar Singer da ke cikin birnin Kano.
Gobarar ta bazu cikin sauri, lamarin da ya haddasa babbar asara ga ’yan kasuwa da iyalansu, inda dukiyoyi masu yawa suka salwanta kafin a samu cikakken ikon shawo kan wutar.
Sanarwar ta bayyana cewa jarin da wahalar shekaru da dama na wasu ’yan kasuwa sun lalace cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan lamari ya jefa jama’a cikin alhini, musamman ganin yadda kasuwar ke da muhimmanci a rayuwar jama'a.

Source: Original
Kabiru Musa Haruna ya ce zuciyar shugabancin KAMCHAFA ta cika da baƙin ciki sakamakon wannan ibtila’i da ya faɗo wa ’yan kasuwa.
Ya kara da jaddada cewa irin wannan gobara na kawo koma baya ga tattalin arzikin kasuwanni da rayuwar talakawa gaba ɗaya.
An mika sakon jaje kan gobarar Kano
Kungiyar ta ce ba ta da cikakken bayani kan ko an samu asarar rayuka ko raunuka sakamakon gobarar ba, sai dai ta bayyana fatan cewa Allah Maɗaukakin Sarki Ya kare rayukan jama’a, ya mayar da alheri.
Kungiyar ta ce:
“A madadin ƙungiyoyin kasuwanni da muke wakilta da daukacin shugabannin KAMCHAFA, muna miƙa saƙon ta’aziyya da cikakken goyon baya ga duk waɗanda wannan iftila’i ya shafa."
Har ila yau, ƙungiyar ta jaddada cewa tana tare da ’yan kasuwar Singer a wannan lokaci mai tsanani, tare da nuna damuwa da alhini kan irin asarar da aka yi.
Ta buƙaci jama’a da hukumomi da su nuna tausayi da haɗin kai domin taimaka wa waɗanda gobarar ta shafa su farfaɗo da harkokinsu.
KAMCHAFA ta roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya sauƙaƙa wannan jarabawa, Ya maye wa ’yan kasuwa abin da suka rasa da mafi alheri.
Gobara ta jawo asara a Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa gobara ta tashi a kasuwar wayoyi da ke Kano a safiyar ranar babbar Sallah, inda ta lalata shaguna da dama tare da jawo asarar miliyoyin Naira ga 'yan kasuwa da dama.
Lamarin ya fara jawo hankalin jama’a ne bayan wani mutum ya wallafa bidiyo a kafafen sada zumunta da ke nuna hayaki mai yawa na tashi daga wani bangare na kasuwar yayin da jama'a ke sabgoginsu.
Wani ɗan kasuwa a Farm Centre mai suna Muhammad Daula ya bayyana cewa mafi yawan masu shaguna ba su je kasuwa ba a ranar saboda bikin Sallah yayin da abin ya faru, wanda ya jawo mutane dawowa duba dukiyoyinsu.
Asali: Legit.ng


