AEDC: Kamfani Ya Sanar da Sabon Farashi da Lokacin Ƙara Kuɗin Lantarki a Garuruwa 4

AEDC: Kamfani Ya Sanar da Sabon Farashi da Lokacin Ƙara Kuɗin Lantarki a Garuruwa 4

  • Kamfanin AEDC ya fitar da sanarwar da tabbatar da cewa za a fuskanci tsadar lantarki a Najeriya
  • Daga ranar 1 ga watan Yulin 2023, farashin da aka saba sayen wutar lantarki daga AEDC zai canza
  • Sabon tsarin canjin kudin kasar waje da bankin CBN ya fito da shi ne ya jawo sauyin da aka samu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kamfanin AEDC mai raba wutar lantarki a Abuja da kewaye ya tabbatar da cewa zai kara farashin da ake shan wuta saboda canjin kudin waje.

A rahoton The Cable, an samu labari AEDC wanda shi ne kamfanin da ke raba wuta zuwa birnin tarayya, Neja, Kogi da Nasarawa zai canza farashinsa.

Jawabin da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi ya bayyana cewa karin farashin ya zama dole ne a dalilin tangal-tangal da Naira take yi a kasuwar canji.

Kara karanta wannan

'Yan Maza Sun Kwanta: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Babban Farfesa a Najeriya Ya Koma Ga Mahaliccinsa

Lantarki
Lantarki zai kara tsada Birnin Abuja Hoto: Getty Images/Ugochukwu Odom
Asali: Getty Images

Bayan zaman Bola Tinubu shugaban kasa, bankin CBN ya bar farashin kudin kasashen waje a hannun ‘yan kasuwa, hakan ya karya darajar Naira.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar da AEDC ya fitar

"Daga 1 ga watan Yulin 2023, a sani cewa za a samu farashin shan wutar lantarki ya tashi sama a dalilin tangal-tangal a kasuwar canji.

A karkashin tsarin MYTO 2022, an tsaida Dalar Amurka ne a kan N441/$1, watakila yanzu dole a daidaita farashin zuwa N750/$1.
Hakan zai yi tasiri a kan farashin da ku ke shan wutar lantarki."

- AEDC

Nawa za a koma sayen wuta?

Daily Trust ta ce ‘yan rukunin B da C da ke samun wuta na awanni 12 zuwa 16 a rana, farashin da za su rika sayen kowane 1kWh zai N100 daga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Akpabio Na Cikin Matsala Yayin da Sanatocin APC 22 Ke Shirin Sauya Sheka Zuwa PDP

Su kuwa gidajen da ke kan rukunin wutar lantarki na A da B da ke yin awanni 16 zuwa 20 da lantarki za su rika biyan farashin da ya zarce N100/kWH.

Ga wadanda ba su amfani da na’urar auna shan wuta, daga Agusta za su ga kudin da za a rika yanko masu a wadannan garuruwa ya canza a dalilin haka.

Dole farashi ya lula sama

Tun a baya mu ka kawo rahoto cewa mutane su shiryawa tashin farashin lantarki na tsakanin 25% zuwa 40% daga ranar Asabar, 1 ga watan Yuli 2023

Yadda aka yi waje da tallafin fetur, hauhawar farashi da sauyin da aka samu a kasuwar canji za su haddasa karin tsadar lantarki a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel