Ministan Tinubu Ya Fadi Shirin Gwamnati kan Magance Rashin Aikin Yi

Ministan Tinubu Ya Fadi Shirin Gwamnati kan Magance Rashin Aikin Yi

  • Matsalar rashin aikin yi ta daɗe tana ci wa mutanen Najeriya musamman matasa waɗanda ke zaman kashe wando tuwo a ƙwarya
  • Ministan ƙwadago da samar da ayyuƙan yi, Muhammadu Dingyadi, ya bayyana cewa gwamnati ta duƙufa wajen ganin ta magance matsalar
  • Ya bayyana cewa an ƙirƙiro shirye-shiryen koyar da sana'o'i domin ganin matasa sun samu abin yi, ta yadda za su iya dogaro da kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Muhammadu Dingyadi, ya yi magana kan matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Muhammadu Dingyadi ya sha alwashin cewa gwamnati ta dukufa wajen magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Ministan kwadago ya magantu kan samar da aikin yi
Muhammadu Dingyadi ya ce gwamnati na kokarin samar da aikin yi Hoto: Muhammadu Dingyadi
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta ce ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan ƙwadago da samar da ayyukan yi, wanda Sanata Diket Plang (APC-Plateau) ya jagoranta a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati na ƙoƙarin magance rashin aikin yi

Muhammadu Dingyadi ya bayyana ƙoƙarin da gwamnati ke yi don shawo kan matsalar rashin aikin yi a ƙasar nan.

Ministan wanda watansa uku kacal da hawa wannan muƙamin, ya jaddada cewa magance rashin aikin yi shine babban aikin da ma'aikatarsa ta sanya a gaba.

"A kowane lokaci, muna aiki ba dare ba rana don magance rashin aikin yi, domin wannan shine babban aikinmu. Duk shirye-shiryenmu na koyon sana'o'i an tsara su ne da manufar rage rashin aikin yi."

- Muhammadu Dingyadi

Dangane da alƙaluman rashin aikin yi a ƙasa, ministan ƙwadagon ya ƙi bayar da wani adadi, inda ya bayyana cewa yana son tabbatar da sahihancin alƙaluman kafin ya faɗe su.

“Ba zan bayar da alƙauman da ba ni da tabbaci a kansu ba. Duk da haka, muna da waɗannan bayanai, kuma hukumomi da ma’aikatu suna aiki tukuru kan wannan batu."

Kara karanta wannan

"Ba kamar Tinubu ba": Amaechi ya fadi yadda ya shirya samar da sauki ga talaka

"Za mu haɗa sahihan alƙaluma mu miƙa su ga kwamitin nan ba da jimawa ba."

- Muhammadu Dingyadi

Ƴan majalisa sun yabi gwamnatin Tinubu

Wasu daga cikin ƴan majalisar dattawan sun yaba da jajircewar gwamnatin Tinubu wajen kula da jin daɗin ma’aikatan Najeriya, waɗanda ke aiki a ƙarƙashin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Sun jaddada cewa aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, wanda ya fara aiki daga 1 watan ga Afrilun, 2024, ya nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da adalci da kyakkyawan yanayin aiki ga ma'aikata.

Gwamnan Bauchi zai rage marasa aikin yi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya shirya ɗaukar ma'aikata domin bunƙasa ɓangaren ilmi na jihar.

Gwamna Bala Mohammed zai ɗauki sababbin malamai 3,000 domin ƙarfafa harkar koyarwa a makarantun sakandire na jihar.

Mutum 2,000 daga cikin sababbin ma'aikatan da za a ɗauka, za su riƙa koyarwa ne a ƙananan makarantun sakandire, yayin da ragowar za su riƙa koyarwa a manyan makarantun sakandire.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng