Kwamishina Ya Fadi Dalilin Maida N100m ga Gwamnatin Abba Gida Gida
- Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarautan Kano, Tajo Othman, ya fadi dalilin maidowa gwamnati kudi
- Kwamitin da gwamnatin Kano ta dora wa alhakin dinka kayan makarantar Firamare da wasu daga cikin daliban jihar
- Amma daga cikin Naira biliyan biyu da aka ware, Kwamitin ya mayar da Naira miliyan 100 ga asusun gwamnatin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano - Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta na Jihar Kano, Alhaji Tajo Othman, ya bayyana dalilin dawo da N100m ga asusun gwamnati.
Kudin sun yi saura daga biliyoyin da aka ware na aikin sayen kayan makaranta da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta rarraba ga daliban makarantun Firamare a jihar.

Asali: Facebook
A cewar Jaridar Daily Trust, kwamishinan wanda ya bayyana haka a yammacin Juma'a ya ce shugabanci na gari irin na Abba Kabir Yusuf ya zama abin koyi ga mabiyansa. Ya ce ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf sun zama darasi gare shi da sauran shugabanni wajen daukar irin wannan mataki na tabbatar da gaskiya, rikon amana da kishin Kano.
Kwamishinan Kano ya yaba wa gwamna Abba Kabir
Jaridar Trust Radio ta ruwaito Tajo Othman ya bayyana cewa bai yi tsammanin Gwamna Kabir Abba Yusuf zai bayyana dawo da miliyoyin Naira da ya yi ga jama’a ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya na ganin Gwamnan ya dauki matakin ne da manufar karfafa wa matasa da sauran al’umma gwiwa wajen kasancewa masu gaskiya da adalci a harkokinsu.
Kwamishinan ya ce:
“A kowanne yanayin shugabanci na gari, shugaba yana zama abin koyi ga mabiyansa.
"Mun fahimci yanayin jagorancin gwamna, kuma mun bi sawunsa. Wannan shi ne abin da ya faru. Burin gwamnan shi ne kowa ya kasance mai gaskiya da adalci gwargwadon iko.”
Abba: Kwamishina ya jinjina wa gwamnan Kano
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta ya yaba wa kyawawan halayen Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen nuna gaskiya da adalci. Ya ce:
“Shi gwamna mai gaskiya ne, don haka mu ma ya kamata mu kasance masu gaskiya. Ban yi tsammanin gwamnan zai bayyana wannan abu ga jama’a ba, amma na yi imani manufarsa ita ce ta gaskiya da karfafawa jama'a.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
"Gwamna Abba ya ba mu amana," Kwamishina
Kwamishinan ya kara da cewa, a matsayinsa na shugaban kwamitin rabon kayan makaranta, gwamnan ya danka masa amanar aikin tare da umartarsu da adalci. Tajo Othman, wanda tsohon jami’in kwastam ne, ya ba da mamaki bayan Gwamna Yusuf ya yaba masa a bainar jama’a kan dawo da N100m da aka yi saura na dinka kayan makaranta.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware Naira biliyan biyu domin aikin samar da kayan makaranta kyauta na yara 798,000 a makarantun firamare na jihar Kano.
Yadda Abba ya yabi gaskiyar Kwamishinansa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa kwamitin da ke kula da rabon kayan makaranta ga ɗaliban makarantun firamare a jihar.
Wannan yabon ya biyo bayan dawowar Naira miliyan 100 da kwamitin ya yi ga asusun gwamnati, daga cikin Naira biliyan 2 da aka ware don aikin, bayan samun rarar kuɗi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng