Sulhu Alheri ne: Dan Majalisar NNPP Ya Fara Gangamin Sasanta Kwankwaso da Ganduje
- Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a hada kai wajen sulhunta Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje
- Alaƙa tsakanin manyan jagororin Kano ta yi tsami na lokaci mai tsawo, lamarin da ya kai ba sa ga maciji da juna bayan canjin gwamnati
- Dan majalisar na NNPP ya shaida cewa wannan matsala ta na jawo koma baya ga ci gaban Kano tare da lalata alakarsu ta addinin Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya fara neman a sulhunta madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Hon. Kofa ya bayyana cewa za a samu tarin alheri a jihar Kano idan har aka samu nasarar gyara alakar da ke tsakanin jagororin biyu, wacce ta dade da yin tsami saboda wasu dalilan siyasa da su ka ratsa tsakaninsu.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Hon. AbdulMumin Kofa ya na ganin rikicin da ke tsakanin Kwankwaso da Ganduje na jawo koma baya a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yana jagorantar wani yunƙuri na ganin an sasanta mutanen biyu, don tabbatar da cigaban jihar da suka taba shugabanta sau biyu kowannensu.
Kofa ya nemi a sasanta Kwankwaso da Ganduje
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Jibrin Kofa ya ce kokarin sulhunta Kwankwaso da Ganduje ba shi da alaka da siyasa ko kokarin mayar da su tafiyar siyasa guda;
Ya ce;
“Duk da za su iya cigaba da kasancewa a cikin jam’iyyunsu daban-daban, ya kamata su duba kansu a matsayin ’yan’uwa.”
Ya bukaci al’ummar Jihar Kano masu kishin cigaba su haɗa kai don ganin an sasanta manyan shugabannin siyasar biyu don amfanin jihar.
“Ganduje da Kwankwaso sun dade tare,” Kofa
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya yi karin haske cewa, Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun dade suna tare a siyasa.
Ya ce:
“Shugabannin biyu sun yi nisa a tafarkin siyasa kuma sun sami nasarori da dama. Kwankwaso ya fara aikinsa a Ma’aikatar Jihar Kano, ya zama Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, kafin ya zama Gwamnan Kano, Minista, da kuma Sanata.
“Ganduje kuwa, wanda shi ma ya fara aikinsa a gwamnati, ya zama Darektan Abuja, Kwamishina, Mataimakin Gwamna karkashin Kwankwaso, kuma Babban Sakataren Hukuma kafin ya zama Gwamnan Kano sannan yanzu Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.
“Ba kowa Allah ke zaba ba don samun irin wadannan damar shugabanci ba.'
Kofa ya jaddada mubaya’a ga Kwankwasiyya
Dan Majalisar NNPP, Dr. AbdulMumin Jibrin Kofa ya jaddada cewa su yaran Kwankwaso ne kuma cikakkun ƴan Kwankwasiyya, amma hakan ba zai hana neman sulhu ba.
Ya ce:
“Dukkanmu mun san cewa mu mabiya ne na Kwankwasiyya kuma mabiyan Sanata Kwankwaso da tafiyarsa. Amma wajibi ne ga wasu daga cikinmu su tabbatar da sulhu tsakanin su.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
“Ko sun yarda ko ba su yarda ba, harkar siyasa daban take; ita zabinsu ce. Amma a matsayinmu na Musulmai, dole mu yi abin da ya dace ta hanyar sulhanta su.
Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi tsokaci kan halin da ake ciki a jihar Kano karkashin mulkin Abba Kabir Yusuf.
Ya kara da tabo Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, inda ya ce tsohon ubangidansa ya rasa magoya baya a Kano, sannan ba zai iya wani kataɓus a zaben 2027 da ke tunkarowa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng